
Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa na cewa an yi kone’kone da sace sace da lalata dukiya a yayin da ake murnar cin kofin Championships League da kungiyar PSG ta yi.
Rahotannin sun kuma ce an kashe mutane 2 yayin murnar sannan an kama sama da 500 da suka aikata laifuka.
Hakanan rahoton yace dansanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai saboda lamarin.
‘Yansanda sun fito da barkonon tsohuwa dan magance wannan matsala ta hatsaniya data kaure.