Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, mutane na cikin wahala da yunwa a Najeriya.
Ya bayyana hakane a legas wajan wani taro da aka gayyaceshi.
Obasanjo yace matsalar tsaro ce ta daidaita kasarnan sannan ya koka da matsalar rashin shugabanci na gari.
Yayi kira ga shuwagabannin kasar da su tashi tsaye wajan inganta rayuwar mutane.
Yace akwai bukatar canja Shuwagabanni wanda zasu kawo ci gaba irin wanda ake bukata.