Friday, December 5
Shadow

Na fita daga Jam’iyyar NNPP>>Inji Abdulmumi Jibrin bayan da NNPP din ta koreshi

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilai, Abdulmumi Jibrin ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, inda ya ce ya amince da matakin korarsa da jam’iyyar ta yi.

Jibrin ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya bayyana cewa bai cancanci kora daga jam’iyyar ba, ba tare an ba shi damar kare kansa ba.

Tun da farko, jam’iyyar ce ta sanar da cewa ta kore shi bisa zarginsa da karya dokokinta.

Ya ce, “na yi mamakin ganin an kore ni daga NNPP. Na yi amannar cewa tattaunar da na yi ba su yi nauyin da za su ja min kora ba,” in shi, inda ya “ban janye komai ba a cikin abin da na fada.”

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Yin ciki a soyayya ba laifi bane, ko da Saurayinki ya taba dirka miki Chiki zai iya aurenki>>Inji Fulbe Gombe

Ya ce ba a gayyace shi ba domin ya kare kansa kan abin da ake zarginsa da aikatawa, “ko a mulkin soja, ana ba wanda ake zargi dama ya kare kansa.”

Ya ce ya so a ce ya ci gaba da zama a jam’iyyar, “Amma tunda jam’iyyar ta kore ni, dole in amince da matakin da ta dauka.”

Dan majalisar ya ce nan gaba kadan zai sanar da matakin da zai dauka a game da makomarsa a siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *