Sanata Ben Bruce ya jinjinawa gwamnatin tarayya kan sakawa yarjejeniyar zuwa duniyar wata hannu tsakanin Najeriya da kasar Amurka.
A jiya ne dai hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya ta tabbatar da cewa, an sakawa yarjejeniyar hannu kuma za’a tura dan Najeriya na farko zuwa sararin samaniyar.
Sanata Bruce yace ya sadaukar da kansa a matsayin dan Najeriya na farko da zai fara zuwa Duniyar watar.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.