Friday, May 1
Shadow

Na yiwa Budurwata chikiy, saidai duk da haka ina sonta, dan hakane na roki iyayena mu je mu baiwa iyayenta hakuri

Wani matashin Bayerabe ya bayar da labarin yanda ya dirkawa Budurwarsa da suka hadu a jami’a ciki.

Yace tun suna ajin farko a jami’a suka fara soyayya a shekarar data gabata, kuma takan je gidansa ta kwana.

Kwatsam sai ta gaya masa cewa ta dauki ciki.

Yace yayi farin ciki amma ita bata yi ba saboda tana tunanin iyayenta ba zasu yaddaba.

Yace ya bata shawarar ta zauna a gidansa har sai ta haihu sai su jewa iyayenta da dan da suka haifa, inda ta amince.

Saidai iyayenta sun samu labarin inda suke zaune inda mahaifinta ya je ya dauketa.

Yace shi kuma yana sonta tunda mahaifinta ya dauketa ya kasa samun nutsuwa.

Karanta Wannan  Lalacewar wutar Lantarki:Majalisa ta gayyaci ministoci dan binciken yanda aka yi da Dala Biliyan $2 da aka bayar da samar da wutar Lantarki

Shine ya je ya samu iyayensa aka je aka baiwa iyayenta hakuri suka hakura, yanzu an ce ya bari idan ta haihu za’a daura musu aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *