
Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta Biyu a Duniya wajan yawan yaran da basa samun Abinci me gina jiki kamar yanda hukumar kula da yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana.
Wakiliyar UNICEF, Nemat Hajeebhoy ce ta bayyana hakan a wajan shirin magance matsalar rashin abinci me gina jiki da ake shiryawa yaran jihohin Adamawa, Borno, da Yobe.
Tace akwai yara guda 600,000 dake fama da matsalar rashin abinci me gina jiki kuma kusan rabinsu na fuskantar kara tsanantar matsalar.
Tace yaran dake fama da matsalar matsananciyar rashin abinci me gina jiki zasu iya mutuwa.