
A ci gaba da wasan neman kaiwa ga gasar cin kofin Duniya, Najeriya ta lallasa Gabon da ci 4-1 a wasan da suka buga da yammacin yau.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jinjinawa ‘yan wasan Super Eagles inda yace su ci gaba da samun Nasara har sai sun kai ga shiga gasar ta cin kofin Duniya.