Wednesday, January 8
Shadow

Najeriya ta naɗa Éric Chelle a matsayin kocin Super Eagles

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa tsohon kocin tawagar Mali, Éric Chelle, a matsayin kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles.

Chelle mai shekara 47 ya jagoranci Mali har zuwa zagayen kwata fayinal a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 a Ivory Coast, kafin mai masaukin baƙi ta doke su.

NFF ta ce ta amince da naɗin nasa ne bayan kwamatinta na musamman ya bayar da shawarar yin hakan a yau Talata.

Naɗin nasa na zuwa ne bayan NFF ta kasa daidaitawa da Bruno Labbadia ɗan ƙasar Jamus game da batun biyan haraji bayan sanar da ba shi aikin a watan Agustan 2024.

Karanta Wannan  Ana neman a binciki matar marigayi tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu kan mutuwarsa

Kafin naɗin nasa, shugaban NFF Ibrahim Musa Gusa ya faɗa wa manema labarai cewa sabon kocin da za su bai wa aikin shi ne zai jagoranci tawagar Super Eagles ta ‘yanwasan cikin gida zuwa gasar kofin Afirka ta CHAN – wadda ake gudanar da wasannin neman gurbi a yanzu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *