Darajar Naira ta dan fara dawowa inda a jiya, Talata aka sayi dalar Amurka akan Naira 1,173 a farashin Gwamnati.
A ranar Litinin dai an sayi dalar akan Naira 1,500 ne a farashin Gwamnatin.
Shi kuwa farashin Pound an saye shine akan Naira 1,888, sai kuma Euro da aka siya akan Naira 1,630.
An sayi dalar Canada akan Naira 1,112.
Sai kuma kudin China, Yuan an sayeshi akan Naira 150.