
Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shakarau ya bayyana cewa shi da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso basa gaba.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi ta kafafen sada zumunta.
Malam Ibrahim Shekarau yace yawanci matsalolin da suka faru tsakaninsa da Kwankwaso ba laifin ko daya daga cikinsu.
Yace misa a APC, NNPP ce ta kawo kaso 60 cikin 100 na wakilan Jam’iyyar daga Kano amma da aka tashi saboda Kwankwaso yana Gwamna sai aka bashi kaso mafi tsoka.
Yace a PDP ma abinda ya faru kenan.
Ya kara da cewa, suna zama inuwa daya da Kwankwaso su tattauna batutuwa.