Sunday, March 23
Shadow

Ni da kwankwaso bama gaba, muna zama Inuwa daya mu tattaunawa batutuwa>>Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shakarau ya bayyana cewa shi da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso basa gaba.

Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi ta kafafen sada zumunta.

Malam Ibrahim Shekarau yace yawanci matsalolin da suka faru tsakaninsa da Kwankwaso ba laifin ko daya daga cikinsu.

Yace misa a APC, NNPP ce ta kawo kaso 60 cikin 100 na wakilan Jam’iyyar daga Kano amma da aka tashi saboda Kwankwaso yana Gwamna sai aka bashi kaso mafi tsoka.

Yace a PDP ma abinda ya faru kenan.

Ya kara da cewa, suna zama inuwa daya da Kwankwaso su tattauna batutuwa.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Kungiyar Gwamnonin Najeriya tace bata yadda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kara harajin VAT ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *