Friday, December 5
Shadow

Ni Musulmi ne kuma nasa Allah a raina sanda nake aiki, Na yiwa Najeriya aiki tukuru ta yanda ko hutu bana samu, kuma a shirye nake na amsa tambayoyin EFCC, amma dai yanzu basu kamani ba ina nan ina hutawa tukuna>>Tsohon Shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari

Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari ya fito ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa wai yana hannun hukumar EFCC inda ake bincikensa.

Kyari ya fitar da sanarwa ta shafinsa na X inda yace a yanzu yana hutawa ne bayan kammala yiwa Najeriya aiki na tsawon shekaru 34.

Yace a lokacin da yake aiki ko hutun sati biyu baya samu dan haka yanzu yana hutun da ya kamata ace yayi a baya.

Yace ‘yan uwa da abokan arziki suna ta kiranshi suna sanar dashi game da wani labari dake cewa an kamashi yana hannun EFCC.

Yace wannan labari karyane, yace a sanda yake aiki ya sa Allah a ransa saboda yasan zai tsaya a gaban Allah ya amsa tambayoyi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Sai yanzu na yadda da masu cewa Sheikh Nura Khalid yana zuwar Wiywiy, inaga kamin yace Sufayene suke fi son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya dan kurbi Shayin Wiywiy din da ya saba sha>>Inji Malam

Dan haka yace a yanzu ma a shirye yake ya amsa tambayoyin EFCC ka yanda ya gudanar da ayyukansa.

Yace ya kamata a daina yada irin wannan labari dan kuwa ba zaiwa masu zuba jari ko masu son zuba jari a Najeriya dadi ba.

Yace ya kamata kafafen yada labarai su rika tantance labari kamin su yadashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *