Wednesday, January 15
Shadow

Nnamdi Kanu na duba yiwuwar yin sulhu da gwamnatin Najeriya

Lauyoyin jagoran ƙungiyar Ipob mai rajin kafa ƙasar Biafra, Nnamdi Kanu sun bayyana cewa akwai yiwuwar su tuntuɓi gwamnati domin neman sasanci a wajen kotu game da shari’ar da ake yi masa.

Ana tuhumar Nnamdi Kanu ne da laifukan da suka jiɓanci ta’addanci a matsayinsa na jagoran ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biafra ta Ipob.

Ƙungiyar na ƙoƙarin ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya ɓalle ne tare da kafa ƙasa mai zaman kanta.

Tuntuni gwamnatin Najeriya ta ayyana ƙungiyar a matsayin ta ƴan ta’adda.

Aloy Ajimakor, wanda shi ne jagoran lauyoyin da ke kare Kanu, ya shaida wa kotu cewa kundin tsarin mulkin Najeriya da dokar da ta kafa Babbar kotun tarayya sun bayar da damar sasantawa a wajen kotu kan duk wani rikici tsakanin mutum da mutum ko kuma wani mutum da gwamnati.

Karanta Wannan  HOTUNA: Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da sauran manyan jami'an gwamnati yayin gabatar da sallar Juma'a yau a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.

Sai dai kotun ta bayyana cewa idan har za a ɗauki irin wannan matakin to wajibi ne ya fito daga ofishin babban mai shari’a na ƙasa, ba daga kotun ba.

Mai shari’a Binta Nyako ta shaida wa lauyoyin Nnamdi Kanu cewa “Kuna da ƴancin tuntuɓar atoni-janar na tarayya idan ya amince da batun sasanci a wajen kotu sai ya shigar da batun gare ni.”

Gwamnatin Najeriya na tsare da Nnamdi Kanu ne tun cikin shekarar 2021 bayan kamo shi daga wata ƙasa tare da mayar da shi cikin ƙasar.

Har yanzu ƙungiyar Ipob na ci gaba da gwagwarmayarta ta neman ɓallewar yankin Biafra duk da cewa shugaban nata na tsare a hannun jami’an tsaro.

Karanta Wannan  Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Ko a cikin watan da ya gabata rundunar sojin Najeriya ta zargi ƴaƴan ƙungiyar da laifin kisan wasu jami’an sojoji a jihar Delta da ke kudancin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *