Monday, June 2
Shadow

Nnàmdì Kanu ya karyata lauyan da ke kare shi ana tsaka da zaman kotu

Nnamdi Kanu ya karyata lauyan da ke kare shi ana tsaka da zaman kotu

An samu ɗambarwa a kotu ranar Talata yayin da shugaban haramtacciyar ƙungiyar, IPOB , Mazi Nnamdi Kanu, ya karyata wani lauya mai suna Charles Ude da ya bayyana kansa a matsayin wanda ke wakiltarsa.

Kanu yana fuskantar tuhume-tuhume da suka shafi ta’addanci a gaban kotu.

A lokacin zaman kotun, alkalin da ke jagorantar shari’ar ya jawo hankalin ɓangarorin da ke cikin shari’ar zuwa wata wasika daga Charles Ude, wanda ya ce shi ne lauya na gaskiya da ke kare wanda ake tuhuma.

Sai dai tawagar lauyoyin da ke kare Kanu sun ce ba su san Ude ba, kuma Kanu da kansa ya tabbatar da hakan, yana mai jaddada cewa Agabi ne kawai lauyansa.

Karanta Wannan  Ku gama hauragiyarku, Tabbas, Babu tantama Tinubu ne zai sake zama shugaban kasa a 2027>>Inji Shugaban APC, Ganduje

Kotu ta kuma tabo batun yawan lauyoyin da ke wakiltar wanda ake tuhuma.

A cewar alkalin, daga cikin lauyoyi 26 da aka lissafa, 16 kawai za su samu damar shiga, yana mai danganta hakan da yarjejeniya da aka riga aka cimma.

“Ina so ku sani, zan iya yanke shawarar ci gaba da shari’ar ta intanet; muna da kayan aikin hakan,” in ji alkalin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *