Thursday, May 8
Shadow

Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a 2031 bayan Tinubu ya gama shiyasa yake son bata min suna>>El-Rufai

Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a shekarar 2031 bayan Tinubu ya gama Mulki.

Yace shiyasa ma Nuhu Ribadun ya hada kai da gwamnan Kaduna na yanzu, Malam Uba Sani dan bata masa suna.

El-Rufai ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.

Inda ya kara da cewa amma kokarin na bata masa suna yana basu wahala.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu da dakataccen Gwamnan jihar Rivers, Sim Fubara sun gana a Landan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *