Thursday, December 18
Shadow
Na fara ganin sakamakon wahalar da kuke sha, Ba zata zama ta banza ba, nan gaba za’a Fanshe>>Shugaba Tinubu

Na fara ganin sakamakon wahalar da kuke sha, Ba zata zama ta banza ba, nan gaba za’a Fanshe>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban ya Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Sakamakon wahalar da 'yan Najeriya ke sha ya fara bayyana. Shugaban ya kuma jinjinawa 'yan Najeriyar bisa nuna dauriya da irin matsin da suka samu kansu a ciki. Shugaban ya bayyana hakane ranar Juma'a a wajan nadin sarautar Olubadan of Ibadanland a garin Ibadan. Tinubu yace wahalar da 'yan Najeriya ke sha saboda tiyatar da yakewa Najeriya ne kuma ba zata zama ta banza ba, nan gaba za'a moreta.
Wallahi Karya nake, kawai ina neman followers ne dan in samu kudin abinci, ina zan kai masa 100>>Inji Mandy Wadda tace zata yi Alfasha da maza 100 saboda ta shiga kundin Tarihin Duniya

Wallahi Karya nake, kawai ina neman followers ne dan in samu kudin abinci, ina zan kai masa 100>>Inji Mandy Wadda tace zata yi Alfasha da maza 100 saboda ta shiga kundin Tarihin Duniya

Duk Labarai
Ayomiposi Oluwadahunsi wadda tace zata yi lalata da maza 100 dan ta samu shiga kundin tarihin Duniya a jihar Legas a yanzu tace da wasa take. Ta bayyana hakane bayan da basaraken Ogun Oba Akintunde Akinyemi yayi kira da a kamata a mata gwajin kwaya sannan a kaita gidan mahaukata. Tace ta yi hakanne kawai dan ta samu mabiya dan kuma ta samu ana bata tallata amma ba zata iya yin lalata da maza 100 ba. https://twitter.com/Teeniiola/status/1971631553232228416?t=Aadoz-syDaUgKCDkcehcqg&s=19
Ana ta kara samun ci gaba a Kannywood:Maryam Yahya ma ta sanar da mallakar sabuwar wayar iPhone 17 pro

Ana ta kara samun ci gaba a Kannywood:Maryam Yahya ma ta sanar da mallakar sabuwar wayar iPhone 17 pro

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahya ta shiga cikin sahun wadanda suka mallaki wayar iPhone 17 pro max a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood. Maryam Yahya ta sanar da mallakar wayar a shafinta na Instagram. Maryam itace ta 3 bayan Ummi Gayu, da Asiya Chairlady da suka sanar da mallakar wayar a baya.
Daga gobe Matatar Man Dangote zata daina sayar da man fetur da Naira

Daga gobe Matatar Man Dangote zata daina sayar da man fetur da Naira

Duk Labarai
Matatar man fetur ta Dangote tace daga yau, zata daina sayar da man fetur dinta da Naira. Ta sanar da cewa man data tanada dan sayarwa a Naira ya kare. Matatar tace hakan ba zai ci gaba ba. Matatar tace wadanda suka bayar da kudinsu dan sayen man da Naira a yanzu suna iya neman a mayar musu da kudadensu. Sannan tace idan an samu chanji aka ci gaba da sayar da man da Naira zasu sanar da abokan hulda.
Baya halatta mace ta aikata Zyna saboda yunwa ko wata bukatar Duniya>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Baya halatta mace ta aikata Zyna saboda yunwa ko wata bukatar Duniya>>Inji Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa yunwa ba uzuri bane ga mace ta aikata zina ko kuma tace wai dan 'ya'yanta su yi makaranta duk bai halatta ba. Yace a guri daya ne kawai ya halatta mace ta aikata Zyna shine idan aka ce za'a kasheta idan bata yadda ba. Malam ya bayyana hakane a wajan karatun da yakevna ranar Juma'a da yamma a masallacin Sultan Bello dake Kaduna, kamar yanda wakilin hutudole ya halarta.
Kalli Bidiyo: Amarya ta dauki hankula saboda yin karatu a wajan Bikinta

Kalli Bidiyo: Amarya ta dauki hankula saboda yin karatu a wajan Bikinta

Duk Labarai
Wannan amaryar data rera karatun Qur'ani a wajan Bikinta ta dauki hankulan mutane sosai inda akai ta muhawara. Wasu sun ce wajan ba muhallin karatun Qur'ani bane inda wasu kuma abinda angon yayi ne ya dauki hankulansu. Irin kallon da angon kewa amaryar yasa mutane ke ta fadar maganganu daban-daban. https://www.tiktok.com/@theluxurious_weddings/video/7553234492324973842?_t=ZS-9030EqUwwTJ&_r=1
Kalli Bidiyo: Itama Asiya Chairlady ta shiga sahun ‘yan matan Kannywood da suka mallaki sabuwar wayar iPhone 17 pro, saidai tace da kudinta ta siya

Kalli Bidiyo: Itama Asiya Chairlady ta shiga sahun ‘yan matan Kannywood da suka mallaki sabuwar wayar iPhone 17 pro, saidai tace da kudinta ta siya

Duk Labarai
Tauraruwar Kannywood, Asiya Chairlady ta bayyana mallakar sabuwar wayar iPhone 17 pro wadda ake yayi. Asiya ta zama ta biyu bayan Ummi Gayu a masana'antar Kannywood da suka fito suka bayyana mallakar wayar a fili. A Bidiyon data wallafa a shafinta na Instagram, an ganta a zaune a shagon da ta sayi wayar. Kalli Bidiyon anan: