Mataimakin shugaban Malawi ya mutu
Mataimakin shugaban ƙasar Malawi, Saulos Chilima ya mutu sakamakon haɗarin da jirgin da ke ɗauke da shi ya yi ranar Litinin.
Shugaban ƙasar ta Malawi, Lazarus Chikwera ya ce "jirgin nasa ya daki dutse" ne inda jirgin ya tarwatse kuma mista Chilima da dukkan waɗanda ke cikin jirgin suka rasu.
An dai samu tarkacen jirgin ne a kusa da wani tsauni.
An dai kwashe awanni ana bincike domin gano jirgin saman da ke ɗauke da mataimakin shugaban ƙasar Malawi.
Jirgin saman ya ɓace ne a ranar Litinin da safe.
Ana tunanin ya faɗi ne a dajin Chikangawa Forest da ke arewacin ƙasar.
Ya fuskanci rashin kyawun yanayi abin da ya sa aka hana jirgin sauka a filin jirgin sama na Mzuzu.
Shugaban Malawi ya ce ya ba da umarnin a ci gaba da aikin ceto mataimakinsa Saulos Chilima har sai an gano ...