Kalli bidiyo: Daliba a jami’ar FUD, dake jihar Jigawa da ta yi cikin shege, ta haihu, ta jefo jaririn da ta haifa daga saman bene
Wata daliba a jami'ar tarayya ta FUD dake Dutse a jihar Jigawa wadda ta yi cikin shege, ta haihu, a kokarinta na boye dan, ta jefo jaririn da ta haifa daga sama.
Lamarin ya dauki hankula inda akaita mata Allah wadai.
Bidiyon faruwar lamarin ya watsu sosai a shafukan sada zuminta inda aka ga wasu na kokarin daukar jaririn da aka jefoshi daga sama.
https://twitter.com/Maxajee/status/1800235143371583952?t=3CGYOgPBd-_Dbeh6ZN4duQ&s=19
Daga karshe dai, An ga cewa, an kama dalibar data aikata wannan danyen aiki.
https://twitter.com/jesuispope/status/1800279994733641950?t=PntT6-RC_XOWfe4Bsi0Msw&s=19
Lamarin yin cikin shege a makarantu, musamman jami'o'i abin dake faruwane a Najeriya, saidai yanda wannan yazo ya baiwa mutane mamaki