Shekara ɗaya maƙiya Kano su ka yi su na cin dunduniyar gwamnatin Abba, Cewa Kwankwaso
Madugun Kwankwasiyya kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya zargi 'yan adawa a Kano da cin dunduniyar gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf har tsawon shekara guda.
Kwankwaso ya fadi haka ne a lokacin da gwamnatin Kano ta ayyana dokar ta-baci kan ilimi a jihar Kano a yau Asabar.
Ya ce, “Bari in fara da taya shi murnar wannan rana mai cike da tarihi, ranar da gwamna ke ayyana dokar ta-baci kan ilimi. Sanin kowa ne cewa gwamna yana aiki tun daga ranar da ya hau mulki a ko’ina a fadin jihar.
“Duk da cewa gwamnan ya na fuskantar kalubale tsawon shekara guda. Nan da nan bayan zaɓe, maƙiyan Jiha sun kai shi Kotu, zuwa Kotun Daukaka Kara zuwa Kotun Koli. Mun ga abin da ya faru duk da sun san cewa babu bukatar a je wata Kotu. Kowa ya san cewa ya ci zabensa...