Wannan wani Bidiyo ne inda aka ga mutane nata rububin daukar hotuna yayin da aka ce Gibirima ya bayyana a bangon wani gini.
Hakan ya farune yayin bikin Maulidi da ya gabata.
https://www.tiktok.com/@kingyahay1/video/7547072216781819153?_t=ZS-8zf0tEIWDeD&_r=1
A baya dai an rika cewa Inyas ko sauran shehunai na darika sun bayyana a jikin bango.
Tauraron me wakar Batsa wanda ya fito daga jihar Sokoto, wanda aka fi sani da Soja Boy ya bayyana cewa hada addini da harkar Nishadi ko rawa da waka Izgili ne.
Ya bayyana cewa Addini da rawa da fim da waka ba zasu taba haduwa ba har abada.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi.
https://www.tiktok.com/@usmansuleyman2/video/7546990774999682312?_t=ZS-8zezVeYgAaH&_r=1
Soja Boy dai yana shan suka sosai a wajan mutane musamman ma kwanannan shine yayi waka da matashiyar 'yar Fim iftihal Madaki wadda aka saba ganinta da Hijabi amma rana daya aka ganta tana rawa da mawaka.
Tauraron fina-finan Hausa, Saheer Abdul da ya je Madina, ibada da sayar da garin Danwake yace da yawan wadanda ke aika masa da neman ya taya su da addu'a matane.
Yace kuma yawanci suna cewa ne ya nema musu addu'ar Allah ya basu mazajen aure wasu kuma suna kiran ya taya su da addu'ar Allah yasa su samu zaman lafiya da mazansu.
Yace irin labaran da matan ke bashi akwai ban tausai.
Ya sha Alwashin taya su da addu'a.
https://www.tiktok.com/@mr_saheeer/video/7548756716633066760?_t=ZS-8zeyAXIqm5w&_r=1
Wata matashiyar Najeriya me suna Faith Joseph ta ki amincewa da yin karuwanci bayan da aka yaudareta aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket.
Matashiyar na aikin gida ne a Afuze, Owan East dake jihar Edo inda aka ce za'a kaita Legas dan ta yi aiki a Supermarket.
Saidai daga baya an tafi da ita kasar Mali, tace sina zuwa aka kaita wajan wata mata wadda Magajiyace, watau uwar Karuwai, data lura da haka sai tace bata yadda ba, ba zata yi ba.
Saidai magajiyar ta gaya mata cewa, aikuwa saidai idan an kawo wata da zata maye gurbinta ne sannan zata iya komawa gida Najeriya.
Matashiya, Faith haka ta zauna har Allah yasa ta lura da wani Ofishin 'yansanda inda ta tsere zuwa can.
Daga baya dai ta samu an dawo da ita zuwa gida Najeriya.
Shugaban hukumar kula da 'y...
Rahotanni daga hukumar bincike ta kasa, The Nigerian Safety Investigation Bureau sun bayyana cewa, an samu biyu daga cikin matuka jirgin saman kamfanin Air Peace da shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Abubuwan da aka samesu da sha shine kwayoyi da kuma giya.
Hakan na zuwane bayan da jirgin da suke tukawa ya kaucewa hanya a filin jirgin samana na Fatakwal a ranar July 13, 2025.
Me magana da yawun hukumar binciken ta Najeriya, Mrs Bimbo Olawumi Oladeji ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai na jaridar Punchng.
An gano cewa matuka jirgin sun yi wasa da rayuwar mutane 103 da suke dauke dasu a wancan lokacin.
Jihar Delta ta yi sabuwar doka game da irin kayan da ya kamata ma'aikatan jihar maza da mata su rika sakawa.
A wata sanarwa data fitar a yau, Alhamis, Jihar tace dolene ma'aikata su rika saka kayan mutunci a yayin da suka je wajan aiki.
Sanarwar tace ana tsammanin maza su rika saka kwat ko riga 'yar ciki su tsuke in banda ranar Juma'a da zasu iya saka kayan gida.
Hakanan ba'a so mutum ya tara gemu da yawa ba aski, ba gyara.
Mata kuma su saka siket wanda zai rika wuce gwiwarsu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta soke harajin Kaso 5 cikin 100 na kamfanonin sadarwa wanda yasa kudin data dana kiran waya suka kara tsada.
Hakan na zuwane daga bakin shugaban hukumar sadarwa ta kasa, NCC, Dr. Aminu Maida inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya bayar da umarnin a yi hakan.
Yace shugaban ya yi hakan ne dan saukakawa 'yan Najeriya da suka fuskanci tsadar kudin kira dana data.
Harajin dai tun bayan kaddamar dashi aka kara kudin kira dana data da kaso 50 cikin 100.
Hakanan jaridar Punchng tace tun a lokacin mulkin Buhari ne aka gabatar da wannan haraji wanda ya samu suka daga kamfanonin sadarwa da masu amfani da wayoyi.
Babban Malamin Addinin Islama, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, da ya kammala aikin gwamnati a watan Mayu na shekarar 2023 ya tattara motocin gwamnati 6 da aka basu yana aiki dasu ya mayarwa da gwamnati kayanta.
Malam yace akwai wani abokinsa da ya gaya mai cewa ba'a mayarwa rikewa ake haka aka saba, saidai malam yace ya nuna masa inda yake rubuce a doka.
Yace indai ba doka bace ta zo dashi a rubuce dan haka shi yana ganin wannan motoci ba halas dinsa bane dan haka ya mayar dasu.
https://www.tiktok.com/@sheihk.prof.panta/video/7547065656139730197?_t=ZS-8zdvu7lHrsX&_r=1
Malam ya bayyana hakane a yayin karatu da yake gabatarwa.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Khadija Osi ta dauki hankula bayan wallafa wannan Bidiyon a shafinta na sada zumunta.
Da yawa dai sun ce hoton Bidiyon bai dace ba saboda yanda ya nuna tsiraicinta.
https://www.tiktok.com/@khadijaosi_/video/7548524389155867910?_t=ZS-8zdv9z6g4WH&_r=1