Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano
Biyo bayan dambarwar data sarkake masarautar Kano, Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya fitar da sanarwa.
Sheikh Dahiru Bauchi ta hannun gidauniyarsa, ya bayyana cewa yana baiwa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Shawarar kada yayi abinda zai kawo hargitsi a jiharsa ta Kano.
Malamin ya bayyana cewa, bai ji dadin abinda gwamnatin jihar Kano ta yi ba na sauke Aminu Ado Bayero ta nada Muhammad Sanusi II ba.
Ya jawo hankalin gwamnatin jihar ta Kano cewa, ta yiwa doka biyayya dan zaman lafiya me dorewa a jihar ta kano.
Shugaban gidauniyar ta Dahiru Bauchi, Ibrahim Dahiruin ya bayyana cewa, babu wanda yafi karfin doka.
Yayi kira ga majalisar majalisar tarayya da ta yi doka da zata hana ‘yan siyasa amfani da damarsu wajan wulakanta sarakai ta hanyar saukesu.
...