Saturday, December 21
Shadow
Ba zan daina fadi ba, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023>>Inji Datti Ahmad

Ba zan daina fadi ba, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023>>Inji Datti Ahmad

Duk Labarai, Siyasa
Mataimakin Peter Obi a takarar shugabancin Najeriya da suka yi a shekarar 2023, Datti Baba Ahmad ya bayyana cewa ba zai daina fada ba cewa, Peter Obi ne ya lashe zaben shekarar 2023. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace a lokacin da ake aikawa da sakamakon zabe ga hukumar INEC an kulle dadamalin yanar gizo da ake aikewa da sakon. Yace aka koma karbar sakon da hannu inda aka juya lamura. Ya kuma kara da cewa jam'iyyarsu a yanzu ta fi jam'iyyar CPC a zaben 2013/2014 karfi nesa ba kusa ba. Ya kara da cewa, tattalin arzikin Najeriya sai kara durkushewa yake, sannan kuma akwai cin hanci da rashawa sosai.
Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Hotuna: Jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja yayi Hadari

Abuja, Duk Labarai, Kaduna
Jirgin kasan dake zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna yayi hadari a yau, Lahadi. Jirgin yayi hadarin ne a daidai Jere. Jirgin ya tashi ne daga Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe 8:05 na safiyar ranar Lahadi. Kuma ya sauka daga kan titinsa a daidai garin Jere. Jami'an tsaron sojoji dana 'yansanda sun je wajan da hadarin ya faru. Hukumar NIBS ta sanar da cewa tana sane da faruwar lamarin kuma ta tura jami'anta zuwa wajan.
Abinda Gwamnatin Kano ta yi, Adalci ne kan rashin adalcin da aka min a baya>>Sarki Muhammad Sanusi II ya gayawa jami’an tsaro

Abinda Gwamnatin Kano ta yi, Adalci ne kan rashin adalcin da aka min a baya>>Sarki Muhammad Sanusi II ya gayawa jami’an tsaro

Duk Labarai, Kano
Me martaba Sarki Muhammad Sanusi II ya bayyanawa jami'an tsaro cewa abinda Gwamnatin jihar Kano ta yi na sauke Aminu Ado Bayero ta mayar dashi kan kujerar sarautar Kano, Adalci ne. Ya bayyana hakane a wani zama da suka yi shi da shuwagabannin jami'an tsaro na Sojoji, DSS, da 'yansanda. Jami'an tsaron sun bayyanawa sarkin cewa, akwai dokar data ce a dakatar da mayar dashi akan kujerar sarautar Kano. Saidai ya bayyana musu cewa, shi bai san da hakan ba, bai ma san da zaman kotun ba, kotun yanar gizo ce. A lokacin da ya karbi takardar sake nadashi sarautar Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa, dama a baya ya fada, Allah ne me bayar da mulki kuma ya karba a lokacin da ya so.
YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

YANZU-YANZU: Kar ka jefa Kano cikin rikicin da ba za a iya gujewa ba, wasu Malaman Musulunci sun gargaɗi Gwamna Abba Kabir Yusuf

Duk Labarai, Kano
Malaman addinin Musulunci da Malaman addinin Musulunci a Jihar Kano, sun gargadi Gwamna Abba Yusuf da ya daina daukar duk wani mataki da zai jefa jihar cikin rikicin da ba za a iya kauce masa ba. Malaman da suka bayar da wannan shawara kan rikicin da ya barke a jihar, sun bayyana muhimmancin kaucewa yanke shawara da ka iya kawo cikas ga al’ummar jihar da kuma kara yiwa al’ummarta nauyi, wadanda tuni suka sha fama da munanan manufofin da suka gabata. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Khalifa Sheikh Lawi Atiku Sanka, Khalifa Mal Abdulkadir Ramadan, Farfesa Abdulahi Pakistan, Malam Yusuf Ahmad Gabari, Lawan Abubakar Triumph, Sheikh Mohd Bakari, Imam Usaini Yakubu Rano, Imam Jamilu Abubakar da Farfesa Ibrahim Mabushira suka sanya wa hannu. Malaman addinin Islama...
Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Duk Abunda ya faru a Kano, Tinubu ne sila>>Inji Atiku

Duk Labarai, Kano
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan yaki ya barke a Kano to shugaban kasa, Tinubu ne sila. Atiku ya bayyana cewa dalili kuwa shine Tinubu ya aika sojoji su je Kano su nada Sarki. Bayan da majalisar jihar Kano ta rushe duka sabbin masarautun da tsohon gwamnan jihar, Umar Ganduje ya kirkiro, an mayar da tsohon sarki, Muhammad Sanusi akan kujerar sarautar Kano inda aka tsige Aminu Ado Bayero. Saidai Aminu Ado Bayero bisa rakiyar sojoji wadanda ake kyautata zaton Gwamnatin tarayya ce ta bashi su ya koma Kano inda ya yada zango a karamar fadar sarki dake Nasara. Shi kuma sabon sarki, Muhammad Sanusi II yana can fada yana karbar mubaya'a daga hakimai da sauran mutanen gari. An dai zargi me baiwa shugaban kasa shawara, Nuhu Ribadu da hannu a...

Amfanin gishiri a gaban mace

Uncategorized
Gishiri na maganin cututtuka wanda bature ke cewa Bacteria. Dan haka ana amfanin dashi wajan magance kaikan gaba na mata kuma yana aiki sosai, wasu ma nan take suke samun saukin kai kayin. Saidai kada a shafa gishiri kai tsaye a kan gaban mace, sannan a lura kada a yi amfani da shirin kwata-kwata idan akwai ciwo a gaban mace. Yanda za'a yi amfani dashi. Idan kina fama da kaikan gaba, ki zuba gishiri a ruwa, idan so samu ne a samu ruwa me dumi, sai a zuba gishiri, kadan. A wanke gaban dashi, kada a zuba ruwan cikin farji. Hanya ta biyi shine, a samu ruwan dumi a zuba madaidaicin gishiri a ciki, sai a zauna a cikin ruwan na tsawon mintuna 15. Da yardar Allah ana samun sauki nan take, wani kuma yakan dan dauki lokaci. Baya ga maganin kaikan gaba, amfani da ruwan gishir...

Namijin Goro: Namijin goro karfin maza

Uncategorized
Namijin Goro sanannen abune da ake amfani dashi a duka fadin Duniya. Akan yi amfani dashi wajan warkar da cutar Mura ko cutar Koda. Namijin goro in English Sunan namijin goro da turanci shine Bitter Kola, ana kuma ce masa Bitter Cola, ko kuma Garcinia Kola. Ana samun Namijin goro a kasashen Afrika kamar su Gambia, Democratic Republic of the Congo, Ivory Coast, Mali, Gabon, Ghana, Liberia, Nigeria, Senegal da Sierra Leone. Kuma masana sun yi bayani sosai akan amfanin da yakewa jikin dan Adam kamar yanda zamu gani a kasa. Amfanin namijin goro Namijin goro na taimakawa masu son rage kiba Yana taimakawa sarrafa abinci. Yana taimakawa garkuwar jiki. Yana saukar da hawan jini. Yana maganin bacin rai da damuwa. Yana maganin guba. Yana maganin ciwon ido. Yan...

Addu’ar janyo hankalin saurayi

Soyayya
A sunnah ta ma'aiki, Sallallahu Alaihi Wasallam babu wata addu'a da aka ruwaito cewa itace ta janyo hankalin saurayi. Saidai zaki iya rokon Allah ya baki soyayyar wane, idan shine Alkhairi. Kuma mafi kyawun hanyar da ya kamata ki bi wajan yin wannan addu'a shine ta hanyar yin Istikhara. Jabir ibn ‘Abd-Allah(RA) ya ruwaito cewa, Manzon Allah, Sallallahu Alaihi Wasallam yana koya mana neman zabin Allah(yin Istikhara) kamar a dukkan al'amuran mu, kamar yanda ake koya mana karatun Qur'ani. Yace duk wanda yake da wata damuwa akan wani abu da yake nema ko yake so to yayi raka'a biyu sai yace "Allahumma inni astakhiruka bi ‘ilmik, wa astaqdiruka bi qudratik, wa asaluka min fadlik al-azim. Fa innaka taqdiru wa la aqdir, wa ta’lamu wa la a’lam, wa anta ‘allamul-ghuyub. Allahumma in kunt...

Maganin Sanyi na gargajiya

Magunguna
Ga masu fama da ciwon Sanyi, a kasa, bayanine na yanda ake maganin ciwon sanyi ta hanyar gargajiya. Da ikon Allah za'a samu sauki, amma idan aka gwada wannan magani bai yi ba bayan kwana biyu, sai a tuntubi likita. ALAMOMIN MACE MEDAUKE DA SANYI1. Jin Zafi Lokacin Jima i2. Kaikayin Gaba3. Fitar farin ruwa agaba4. Gushewar Shaawa5. Warin GabaALAMOMIN SANYI NA MAZA1. Kankancewar Gaba2. Saurin Inzali3. Kaikayin Matse matsi4. Kaikayin Gaba5. Gushewar Shaawa6. Da Sauransu. Yadda ake maganin Sanyi WATO ( INFECTIOS )1- A samu namijin goro guda 5,2- a samu citta mai ashar (mai yatsu) guda 4, ko 53- a samu tafarnuwa guda 3 a ko 4 ajajjaga su,4- lemon tsami guda 5,Sai ayanka su kanana Kuma a jajjaga su,Shikuma lemon tsamin ayanka shi amatsa ruwan acikin tukuya Kuma ajefa bawon aciki ataf...