Saturday, July 13
Shadow

Amfanin gishiri a gaban mace

Gishiri na maganin cututtuka wanda bature ke cewa Bacteria.

Dan haka ana amfanin dashi wajan magance kaikan gaba na mata kuma yana aiki sosai, wasu ma nan take suke samun saukin kai kayin.

Saidai kada a shafa gishiri kai tsaye a kan gaban mace, sannan a lura kada a yi amfani da shirin kwata-kwata idan akwai ciwo a gaban mace.

Yanda za’a yi amfani dashi.

Idan kina fama da kaikan gaba, ki zuba gishiri a ruwa, idan so samu ne a samu ruwa me dumi, sai a zuba gishiri, kadan.

A wanke gaban dashi, kada a zuba ruwan cikin farji.

Hanya ta biyi shine, a samu ruwan dumi a zuba madaidaicin gishiri a ciki, sai a zauna a cikin ruwan na tsawon mintuna 15.

Karanta Wannan  Maganin kaikan gaba da kurajen gaba na mata da maza

Da yardar Allah ana samun sauki nan take, wani kuma yakan dan dauki lokaci.

Baya ga maganin kaikan gaba, amfani da ruwan gishirin na kuma bada kariya na hana kananan cutuka zama a gaban mace.

A kiyaye, kada a yi amfani da dabulu, ko wasu mai da ba likita yace a yi amfani dasu ba wajan wanke gaban mace, yin hakan ka iya kara yawan kaikan da ake ji.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *