Monday, April 20
Shadow
Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai sauke Badaru daga Ministan Tsaro ya baiwa Janar Christopher Musa

Da Duminsa: Shugaba Tinubu zai sauke Badaru daga Ministan Tsaro ya baiwa Janar Christopher Musa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Tinubu na shirin sauke Muhammad Badaru daga ministan tsaro. Inda zai maye gurbinsa da tsohon shugaban sojoji Janar Christopher Musa. Kafar Daily Nigerian ce ta bayyana hakan a wani Rahoto da yammacin yau, Litinin. Hakan na zuwane bayan da aka ga tsohon shugaban sojojin ya kai ziyara fadar shugaban kasa
Gwamnatin Kano ta jaddada aiwatar da dokar hana sana’ar achaɓa a jihar

Gwamnatin Kano ta jaddada aiwatar da dokar hana sana’ar achaɓa a jihar

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da jaddada aiwatar da dokar hana sana'ar achaɓa ta shekarar 2013, wani mataki da ta ce zai taimaka wajen kare tsaro da rage laifuka, da tabbatar da doka da oda a fadin jihar. Ma’aikatar Shari’a ta bayyana cewa dokar, wadda ta dade tana nan daram kuma za a ci gaba da aiwatar da ita sosai. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da babban mai bai wa gwamnan jihar Shawara Kan Harkokin Labarai na Ma’aikatar Shari’a ya fitar Babban lauyan jiharkuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya buƙaci jama’a musamman masu baburan haya wata acaɓa da su yi biyayya ga tanade-tanaden dokar. Ya tunatar da cewa “Dokar ba sabuwa ba ce, kuma dole a kiyaye ta domin amfanin kowa da kowa.” A cewarsa, gwamnatin jihar ba za ta lamunci karya dokar ba, mus...
Kalli Bidiyon: Bidiyon na hadu da Wata Bafulatana me tallar Nono na tambayeta waye Dahiru Usman Bauchi a wajensu, Sai Tace Allah ne(Subhanallahi)

Kalli Bidiyon: Bidiyon na hadu da Wata Bafulatana me tallar Nono na tambayeta waye Dahiru Usman Bauchi a wajensu, Sai Tace Allah ne(Subhanallahi)

Duk Labarai
Malam ya bayyana cewa ya hadu da wata bafulatana me sayar da nono inda ya tambayeta waye Dahiru Bauchi a wajansu? Sai tace masa Allah ne( Subhanallahi) Malam yace idan haka bata faru ba kada Allah ya bashi abinda yake nema Duniya da Lahira. https://www.tiktok.com/@jan_zaki03/video/7578886793613823240?_t=ZS-91rbJEAReTZ&_r=1
Da Duminsa:Kalli Bidiyon yanda matasa suka fito suka ce sai ‘yansanda sun basu Tshàgyèràn Dhàjìn da aka kama sun Shyekye shi a Kano

Da Duminsa:Kalli Bidiyon yanda matasa suka fito suka ce sai ‘yansanda sun basu Tshàgyèràn Dhàjìn da aka kama sun Shyekye shi a Kano

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, an kama wani Tshàgyèràn Dhàjì a Kofar ruwa. Inda aka wuce dashi Goron Dutse. Saidai matasa sun fito suna zanga-zanga inda har suka kona taya akan titi suna cewa sai an basu me laifin sun kasheshi https://twitter.com/SaharaReporters/status/1995533118078324891?t=PGjkecebrY5ZcEMyfpiohw&s=19
Ba zan taba yin Sulhu da Tshàgyèràn Dhàjì ba>>Inji Gwamnan Kaduna

Ba zan taba yin Sulhu da Tshàgyèràn Dhàjì ba>>Inji Gwamnan Kaduna

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya bayyana cewa, ba zai taba yin sulhu da tsageran daji ba. Yace zasu tsaya tsayin daka dan tabbatar sun kwatarwa wadanda ayyukan tsageran daji suka saka a halin matsin rayuwa. https://twitter.com/Waspapping_/status/1995483288517988594?t=Fg3S06ongVaNwkUJZnhVpQ&s=19 Hakan na zuwa ne bayan da a baya, Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya zargi Gwamnatin jihar Kadunan da biyan tsageran dajin Naira Biliyan 1.
Kalli Bidiyon Gwamnin Ban tausai inda Hukumomin sojan Najeriya suka kama wani soja me mukamin Kanal saboda yayi korafin an ki kara mai matsayi zuwa Brigadier General

Kalli Bidiyon Gwamnin Ban tausai inda Hukumomin sojan Najeriya suka kama wani soja me mukamin Kanal saboda yayi korafin an ki kara mai matsayi zuwa Brigadier General

Duk Labarai
Wannan Bidiyon wani soja ne gwanin Ban Tausai inda aka ganshi an aika sojoji su kamashi saboda yayi korafin an ki kara masa mukami. Sojan dai na da mukamin Kanal ne inda yake neman a kara masa mukami zuwa Brigadier Janar amma yace shekara da shekaru an ki a masa karin mukamin. An ga 'ya'yansa na ta kururuwa yayin da ake tafiya dashi. https://twitter.com/SaharaReporters/status/1995489166768160960?t=6MDKizrTjD5ueM7gUDiBbQ&s=19
Ba zaman taba bari a ci gaba da haka ba, dole Tinubu ya canja Shettima ya dauko Kirista >>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Ba zaman taba bari a ci gaba da haka ba, dole Tinubu ya canja Shettima ya dauko Kirista >>Inji Rev. Ezekiel Dachomo

Duk Labarai
Malamin Kirista, Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa Mulkin musulmi da Musulmi da ake yi a Najeriya ya isa zama cin zarafi na karshe ga Kiristocin kasarnan. Yace dolene Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sauke Kashim Shettima ya dauki Kirista a matsayin mataimaki. Yace ba zai bari abubuwa su ci gaba da zama a haka ba dan kuwa nan gaba jikokinshi zasu iya komawa musulmai kuma ba zai so haka ba. https://twitter.com/channelstv/status/1995415057606271153?t=eSClaCFwX65qbNnNapFHmQ&s=19