Wednesday, March 4
Shadow
Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina

Duk Labarai
Gwamna Dikko Raɗɗa zai fara biyan Limaman Coci alawus-alawus, zai ɗauki Malaman da za su karantar da addinin kiristanci a Katsina. Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da bayar da alawus-alawus ga Limaman Coci a matsayin wani ƙoƙari na haɗin kai a addinai da kuma bayar da gudummawa ga Malaman addinai. Ƙungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Katsina ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da sakataren Kungiyar Dakta Musa Daniel Danladi ya fitar a madadin Shugaban Ƙungiyar Very Rev. Fr. Richard Shuaibu Liti. Haka zalika, yace Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya amince da ɗaukar Malaman da suka karanci addinin kiristanci domin karantarwa a makarantun gwamnati, inda Kungiyar CAN ta bayyana cewa hakan zai tabbatar da daidaito da ci gaba, tana mai cewa ƙungiyar ta daɗe tana neman haka. Usman...
Kalli Bidiyo: Yanda mutane suka rikawa motocin ‘yan siyasa rotse da duwatsu a Zaria, Kaduna

Kalli Bidiyo: Yanda mutane suka rikawa motocin ‘yan siyasa rotse da duwatsu a Zaria, Kaduna

Duk Labarai
An ga Bidiyon yanda aka rikawa motocin 'yan siyasa rotse a Zaria jihar Kaduna. An ji matasa na fadin bama so, bamayi. Saidai kowane bangare tsakanin APC da ADC na ikirarin cewa abokan hamayarsa ne akawa hakan, wasu na cewa 'yan APC ne akawa haka yayin da wasu ke cewa 'yan ADC ne akewa hakan. A ranar Asabar ne dai za'a gudanar da zabe a wasu bangarori na jihar. https://twitter.com/Abdullahigoslow/status/1956099059267027228?t=SWVNuTEqjxCd79sLJH6lng&s=19 Akwai adawa me zafi tsakanin Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad da Gwamna me ci, Malam Uba Sani.
Kalli Bidiyo: Inda Gwamna Abba Kabir Yusuf yace yana bayar da Naira Dubu 50 a rika baiwa matasa duk wata a wajan wani taro da ya halarta, saidai matasan sun ce ba’a basu ko sisi

Kalli Bidiyo: Inda Gwamna Abba Kabir Yusuf yace yana bayar da Naira Dubu 50 a rika baiwa matasa duk wata a wajan wani taro da ya halarta, saidai matasan sun ce ba’a basu ko sisi

Duk Labarai
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa daya daga cikin ayyukan da yakewa jihar Kano Shine baiwa matasa tallafin Naira dubu 50 a wata. Ya bayyana hakane a wajan wani taron siyasa. Saidai matasan sun musanta wannan ikirari na gwamnan inda suka ce ba'a basu ko sisi. Gwamnan dai yace zai yi bincike kan lamarin.
Matsalar tsaro ta janyowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 7.17 sannan kaso 40 na dabbobin da ake dasu sun salwanta saboda matsalar

Matsalar tsaro ta janyowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 7.17 sannan kaso 40 na dabbobin da ake dasu sun salwanta saboda matsalar

Duk Labarai
Wata Kungiya me sun, Agramondis Research and Consulting ta bayyana cewa matsalar Tsaro ta jawowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 7.17 sannan kaso 40 cikin 100 na dabbobin da ake dasu sun salwanta. Rahoton yace bangaren dabbobi na taimakawa da kaso 10 cikin 100 na ci gaban Najeriya sannan ya samarwa mutane Miliyan 4.5 aikin yi amma gwamnati bata zuba jari sosai a bangaren. Kungiyar tace fari, Canjin Yanayi da matsalar tsaro, da karancin ruwan sama da rikicin manoma da makiyaya na kawowa bangaren tsaikon ci gaba. Dan hakane ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo dauki a hangaren ta hanyar ilimantar da manoma da makiyaya da basu tallafi da kayan aiki na zamani
Gwamna Abba Kabir Ya Baiwa Matashin Yaro Mai Harkar Kere-Kere A Kano Jari Na Makuden Kudade Tare Da Daukar Nauyin Karatunsa

Gwamna Abba Kabir Ya Baiwa Matashin Yaro Mai Harkar Kere-Kere A Kano Jari Na Makuden Kudade Tare Da Daukar Nauyin Karatunsa

Duk Labarai
Gwamna Abba Kabir Ya Baiwa Matashin Yaro Mai Harkar Kere-Kere A Kano Jari Na Makuden Kudade Tare Da Daukar Nauyin Karatunsa. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Hazikin matashin nan mai harkar kere-kere, Injiniya Khalifa, ya samu tallafin makuden kudade daga wurin Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf domin ci gaba da harkar kere-kerensa kamar yadda ya jima yana ta neman jari. Haka kuma Gwamna zai dauki nauyin ci gaba da karatunsa. Daga Fauziyya D. Sulaiman
Kalli Hotuna: Yanda Sakkwatawa suka fito da yawa suka tarbi Tsohon Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal bayan sakoshi daga hannun EFCC

Kalli Hotuna: Yanda Sakkwatawa suka fito da yawa suka tarbi Tsohon Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal bayan sakoshi daga hannun EFCC

Duk Labarai
Sakkwatawa da yawa ne suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka nunawa tsohon Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal soyayya bayan da ya koma jihar bayan sakoshi daga hannin EFCC. Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya shafe kwana daya a hannun EFCC inda suke zarginsa da cire Naira Biliyan 189 daga asusun bankin jihar ba bisa ka'ida ba. ADC ta yi zargin cewa, Bita da kullin siyasane yasa EFCC kama tsohon Gwamnan.
Kalli Bidiyon wani dan Izala da yaje Maulidi a kasar China, sabosa irin kayan abincin da aka shirya a wajan

Kalli Bidiyon wani dan Izala da yaje Maulidi a kasar China, sabosa irin kayan abincin da aka shirya a wajan

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Wani dan Najeriya da yace ba ruwansa da Maulidi a Najeriya, da ya je kasar China ya halarci Maulidi saboda irin yanda aka shiryashi. An ganshi a wajan Maulidin yana cin kayan abinci kala-kala. Da yawa dai sun ce da haka ake Maulidi a Najeriya da yawa sun rika halarta. https://www.tiktok.com/@elbildad/video/7538087905353305350?_t=ZS-8ytN08Tjp1U&_r=1