Thursday, March 5
Shadow
Da Duminsa: Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi aure, Ji bayani game da wanda ta aura, a ina aka daura

Da Duminsa: Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi aure, Ji bayani game da wanda ta aura, a ina aka daura

Duk Labarai
Rahotanni na bayyana cewa an ɗaura auren jaruma Rahama Sadau a Kaduna a yau Asabar. Wasu makusantan ta sun tabbatar da daura auren a masallacin Masallacin Atiku Auwal Unguwan Rimi, tare da angonta Ibrahim Garba. An ɗaura auren ne kan sadaki Naira 300,000. Abokan sana'arta da suka hada da Ali Nuhu, Hassan Giggs da Maryam Booth duka sun tayata murna.
Idan PDP ta yi nasarar shawo kan tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2027, babu wanda zai iya kayar dashi>>Sule Lamido

Idan PDP ta yi nasarar shawo kan tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya tsaya takara a 2027, babu wanda zai iya kayar dashi>>Sule Lamido

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne ya fi dacewa da zama ɗan takarar jam'iyyar PDP a babban zaɓen shekarar 2027, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da su yi duk mai yiwuwa wajen jawo hankalin tsohon shugaban a kan ya koma jam'iyyar ya tsaya takara. "Ina tunanin ya kamata PDP ta janyo shi: shi ne ya fi dacewa ya mata takara. Duk wani ɗantakara da PDP za ta tsayar, ƴan Najeriya za su zaɓe shi," in ji tsohon gwamnan kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da tashar Channels. Lamido ya bayyana Jonathan a matsayin wanda ya fahimci ƙasar kasancewar ya yi mulki a baya, kuma ya san yadda zai yi mu'amalanci mulkin ƙasar. Ya ce ba su da wani ɗantakara daga kudancin Najeriya da ya fi tsohon shugaban ƙasar idan ana b...
Fasto Adeboye ya bayyana ranar da zai koma ga Allah

Fasto Adeboye ya bayyana ranar da zai koma ga Allah

Duk Labarai
Babban Faston Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya sake bayyana hasashe kan yadda zai rabu da duniya. Ya ce zai mutu cikin lumana, a ranar Lahadi, bayan ya halarci cocin kuma ya ci sakwara, abincin da yafi so. Da ya ke jawabi a rana ta huɗu na babban taron cocin na kasa da kasa mai taken “The Overcomers”, Fasto Adeboye ya jaddada cewa mutuwa ba sai da ciwo ba. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Faston ya taba bayyana wannan hasashen shekaru biyu da suka gabata, inda ya ce: “Zan mutu ne a ranar Lahadi, bayan na halarci coci, na ci sakwara da nake so, sannan in rabu da duniya ba tare da wani ciwo ba.” Faston ya ce mutuwarsa za ta kasance ta gaggawa kuma salin-alin zai mutu.
Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyan 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba”>>Inji Gwammati

Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyan 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba”>>Inji Gwammati

Duk Labarai
"Gidajen Talakawa Milyan Biyar Ne Suka Amfana Da Tallafin Naira Bilyqn 493 Da Shugaba Tinubu Ya Raba". Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire takunkumin da aka saka kan asusun Hukumar Shirin Zuba Jarin Jin Kai ta Ƙasa “National Social Investment Programme Agency (NSIPA)”, wanda ya kai ga sakin sama da Naira biliyan 493 domin tallafawa gidaje miliyan biyar a fadin ƙasar. Tun a ranar 8 ga Janairu, 2024 ne aka dakatar da Ministar Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr Betta Edu, tare da umartar Hukumar Yaƙi da Laifukan Tattalin Arziki da Kuɗi (EFCC) ta gudanar da bincike kan duk wasu harkokin kuɗi na ma’aikatar da hukumomin da ke karkashinta. Haka kuma, Shugaban Ƙasa ya kafa kwamiti karkashin jagorancin Ministan Kudi, Wale Edun, domin duba tsarin kuɗi na shirin jin kai da inganta shi do...
YADDA ƳAN SANDA SUKA KAMA NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR

YADDA ƳAN SANDA SUKA KAMA NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR

Duk Labarai
“YADDA ƳAN SANDA SUKA KAMA NI, BA TARE DA SANIN CEWAR NINE KWAMISHINAN ƳAN SANDA BA” – MD ABUBAKAR. “A lokacin da nake Kwamishinan Ƴan Sanda a jihar Lagos, bana wasa da aiki — musamman ranar Asabar. Ko da yake ayyuka na suna farawa ne daga karfe 10 na safe, wannan rana na tashi tun 6 na safe don in kai ziyara ba tare da sanarwa ba. Na hau motata Jeep na nufi ofis, amma sai na yanke shawarar yin ‘yin ziyarar ba-zata’ ga wasu 'yan sanda a kan hanya – domin in ga irin yadda suke gudanar da aikinsu. A wani shingen bincike “checkpoint” dake titin Herbert Macaulay, wasu matasan 'yan sanda suka tsaida ni. Wani karamin dan sanda (constable) ya kalle ni yace: "Kai saurayi, ina zaka ne da motar mahaifinka?" Ya bukaci takardun motar da shaidar lasisin tuƙi. Na ce masa sunana Moha...
PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu a 2027

PDP ta gargaɗi mambobinta kan goyon bayan Tinubu a 2027

Duk Labarai
Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta gargaɗi mambobinta da ke nuna goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu na APC a 2027. Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam'iyyar Hon. Debo Ologunagba ya fitar, PDP ta bayyana hakan da ta ce wasu mambobinta na yi a matsayin yi mata zagon-ƙasa. ''Abin taƙaici ne abinda wasu mambobinmu ke yi a kafafen yaɗa labarai, inda maganganunsu da ayyukansu ke nuna goyon baya ko yin wani abu da bai wa ɗan takarar APC nasara a zaɓen 2027,'' a cewar sanarwar. PDP ta ce hakan ya saɓa wa dokokin da suka kafa jam'iyyar, kuma barazana ce ga ci gaba da wanzuwar jam'iyyar. Jam'iyyar ta kuma ce hakan zai kawo tarin matsalolin da za su haifar da rarrabuwar kawuna a cikinta, wanda kuma cewarta idan ba a magance su ba za su janyo wa jam'iyyar rashin ...