Thursday, March 5
Shadow
Da kasuwancina na habaka sosai, bankuna sun rika aikomin tsala-tsalan ‘yan mata dan in mayar da kudin ajiya ta can>>Inji Attajirin Najeriya, Femi Otedola

Da kasuwancina na habaka sosai, bankuna sun rika aikomin tsala-tsalan ‘yan mata dan in mayar da kudin ajiya ta can>>Inji Attajirin Najeriya, Femi Otedola

Duk Labarai
Attajirin Najeriya, Femi Otedola ya bayyana cewa a lokacin kasuwancinsa na habaka sosai, bankuna suna aika mata kyawawan 'yan mata dan su ja hankalinsa ya mayar da ajiyar kudi acan. Ya bayyana hakane a wani littafin tarihin rayuwarsa da yanda ya gudanar da kasuwanci da yake shirin wallafawa wanda jaridar TheCable tace ta samu gani. Yace ya samu matsala bayan da ya saro man fetur daga kasashen wajan lokacin man yana a farashin Dala $140 amma aka samu tsaiko be karaso Najeriya ba sai da ya koma farashin dala $40. Yace hakan ya jefashi cikin matsanancin bashi. Hakanan yace karya darajar Naira ma ya kara jefashi cikin wahala sosai. Yace a lokacin da bashin bankin ya mai yawa kuma sai bankin suka koma aika masa da jigba-jibgan mazaje masu fadin kirji dan su bashi tsoro ya biya.
Da Duminsa:Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sauka a Akure wajan taron tallafawa kananan masana’antu

Da Duminsa:Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sauka a Akure wajan taron tallafawa kananan masana’antu

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim shetty ya sauka a garin Akure jihar Ondo inda yake ziyarar aiki wajan taron kaddamar da tallafawa kananan masana'antu. Me magana da yawun Kashim Shettima, Stanley Nkwocha, ya tabbatar da hakan inda yace Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa dana Ekiti, Biodun Oyebanji da sauran manyan jami'an gwamnati ne suka tarbi Kashim Shettima a filin jirgin. An shirya taron ne dan tallafawa kananan masana'antu a matsayin ginshikin ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Kalli Bidiyon Barnar kudi: Yanda Titin Legas zuwa Calabar da Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira Tiriliyan 15 akai ya fara lalacewa tun kamin a kammalashi

Kalli Bidiyon Barnar kudi: Yanda Titin Legas zuwa Calabar da Gwamnatin Tinubu ta kashe Naira Tiriliyan 15 akai ya fara lalacewa tun kamin a kammalashi

Duk Labarai
Bidiyo ya bayyana na titin Legas zuwa Calabar wanda Gwamnatin tarayya ta kashe Naira Tiriliyan 15 akanshi wanda kuma ya fara lalacewa. Wanda ya dauki Bidiyon ya nuna yanda ba'a gina Makwararar ruwa a gefen titin ba wanda hakan ya fara kawo zaizayar kasa titin na lalacewa. https://twitter.com/omoelerinjare/status/1952502828662132988?t=_gFpF8_OVZli6WfLIam3cg&s=19
Kalli Bidiyo: Ku rufawa kanku Asiri kada ku shiga aikin Soja, Wani sojan Najeriya ya gargadi matasa

Kalli Bidiyo: Ku rufawa kanku Asiri kada ku shiga aikin Soja, Wani sojan Najeriya ya gargadi matasa

Duk Labarai
Wani sojan Najeriya ya gargadi matasa da cewa su rufawa kansu Asiri kada su shiga aikin soja. Yace aikin ba dadi kuma ba'a wa sojojin Adalci, domin kuwa suna bautawa kasarsu ne amma kasar bata damu dasu ba. Sojan ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1952421319493951945?t=TdaI_dOy4snO17Jp2gQBvQ&s=19
Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC inda shuwagabannin jam’iyyar na jihohi suka hada kai suka ce basu yadda da su Atiku da Peter Obi ba

Sabon Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC inda shuwagabannin jam’iyyar na jihohi suka hada kai suka ce basu yadda da su Atiku da Peter Obi ba

Duk Labarai
Shuwagabannin jam'iyyar ADC na jihohi sun hade kai inda suka ce basu yadda da shugabancin David Mark a matsayin shugaban rikon kwarya na jam'iyyar ba. Hakan na zuwane a wata sanarwa da shugaban kungiyar tasu me suna,Amb. Elias Adokwu ya sakawa hannu tare da sa hannun sakataren watsa labarai na kungiyar, Godwin Alaku. Sun bayyana cewa hadakar 'yan Adawa ta su Atiku karfa-Karfa ta musu. Sun ce kuma hakan ya sabawa dokokin jam'iyyar.
Kai Duniya: Ji yanda aka kama ‘ya’ya mata 2 ‘yan uwan juna da suka shirya yiwa mahaifinsu Damfarar Naira Miliyan 5 A Abuja

Kai Duniya: Ji yanda aka kama ‘ya’ya mata 2 ‘yan uwan juna da suka shirya yiwa mahaifinsu Damfarar Naira Miliyan 5 A Abuja

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan babban birnin tarayya, Abuja ta kama wasu mata 2 'yan uwan juna bisa shirya garkuwa da daya daga cikinsu dan su damfari mahaifinsu Naira Miliyan 5. Mahaifin nasu me suna Mr. Innocent ne da kansa ya kai karar bacewar diyarsa, Miss Leadway Innocent 'yar Kimanin shekaru 16 wadda yace tun da ta tafi rubuta jarabawa a Government Secondary School, Karu bata koma gida ba. Ya kai karar ne ranar 30 ga watan Yuli 2025 inda yace tun ranar 18 ga watan na Yuli diyar tasa ta bace. Kakakin 'Yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace mahaifin ya kai korafinne a ofishin 'yansanda dake Jikwoyi Division. Yace daga baya an kirashi inda aka ce an yi garkuwa da diyar tasa ne ana neman ya biya kudin fansa. Tace hukumar 'yansanda ta bazama bincike...
Kalli Bidiyon: Teema Sadau da Saleem Goje sun yi karin haske kan maganar cewa, sun yi aure

Kalli Bidiyon: Teema Sadau da Saleem Goje sun yi karin haske kan maganar cewa, sun yi aure

Duk Labarai
A yayin da labarai suka karade kafafen sadarwa cewa Kanwar Rahama Sadau, Fatima Sadau ta yi aure kuma Saleem Goje shine angon, duka su biyun sun fito sun yi karin haske kan lamarin. Teema tace an Mata aure a Tiktok, saidai tace ba gaskiya bane tace idan lokaci yayi za'a sani. Ta yi wannan bayanine a Bidiyon da aka ganta tare da 'yar uwarta. https://www.tiktok.com/@hausa.comedy8/video/7534998019691777285?_t=ZS-8ycWxfwcSlk&_r=1 Shima Dai Goje akwai murya dake yawo a kafafen sadarwa inda ake dangantashi da ita cewa tashi ce, yace bai auri https://www.tiktok.com/@fagen_kannywood._/video/7534870742643608837?_t=ZS-8ycYrFYzQw5&_r=1 Wannan labari dai ya dumama kafafen sadarwa sosai.
Nafisa data lashe gasar Turanci ta Duniya ta cancanci kyautar Dala 100,000 da gida da lambar OON>> Inji Farfesa Pantami

Nafisa data lashe gasar Turanci ta Duniya ta cancanci kyautar Dala 100,000 da gida da lambar OON>> Inji Farfesa Pantami

Duk Labarai
Nafisa ta cancanci kyautar Dala 100,000 da gida da lambar OON - Farfesa Pantami Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa Nafisa Abdullahi wadda ta lashe gasar Turanci ta duniya ta cancanci kyautar Dala 100,000 da kuma gida da lambar yabon OON. Pantami ya bayyana haka a wani rubutu da ya wallafa a yau Talata a shafinsa na Manhajar Facebook.
Zuwa yanzu, Ahmed Musa ne kadai ya cika alkawarin da yayi na bayar da gudummawar Naira Miliyan 5 a wajan Bikin Tauraron Kannywood, Jamilu Kochila, kalli Rasit

Zuwa yanzu, Ahmed Musa ne kadai ya cika alkawarin da yayi na bayar da gudummawar Naira Miliyan 5 a wajan Bikin Tauraron Kannywood, Jamilu Kochila, kalli Rasit

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa shine na daya wajan cika Alkawarin gudummawar kudi a wajan bikin tauraron Kannywood, Jamilu Kochila. Ahmed Musa, yayi alkawrin bayar da Naira Miliyan 5. Kuma a jiya, Mansurah Isah ta wallafa Rasit din shaidar cika alkawarin da yayi. Mansurah ta kara da cewa zasu fara wallafa sunan wadanda suka cika Alkawarin da suka dauka. Saidai itama Sadiya Kabala ta bayyana cewa, Daga yanzu idan aka je wajan Biki zata tashi tace ta bada gummawar Naira kaza sai ta yi fuska kawai. Hakan dai alamu ce dake nuna cewa, da yawa basu cika alkawuran da suka dauka a wajan bikin ba.