Friday, December 19
Shadow
Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Facebook da Instagram na barazanar daina aiki a Najeriya saboda Harajin da Gwamnatin Tinubu ke saka mai yayi yawa

Duk Labarai
Kamfanin Meta iyayen Facebook da Instagram na barazanar ficewa daga Najeriya saboda yawan dokokin da gwamnatin tarayya ke gindaya musu. Hakanan dayan dalilin da yasa kamfanin ke son ficewa daga Najeriya hadda harajin da ake kaka ba musu wanda suka ce yayi yawa. Gwamnatin Najeriya ta maka kamfanin META a kotu akan zarge-zarge daban-daban inda take neman kamfanin ya biyata diyyar Dala Miliyan $290m, META sun shiga kotu amma basu yi nasara ba. Kamfanin na Meta dai shine kuma ke da manhajar WhatsApp amma bai bayyanata cikin wanda zai kulle ba. Kotun dai ta baiwa kamfanin nan da zuwa watan Yuni ya biya harajin da aka kakaba masa.
Bidiyo Kalli Miliyan 10 da kayan Abinci, Shinkafa, Kaza, da Talotalo, lemu da za’a kai a matsayin kudin fansa dan kubutar da wani da aka yi Gàrkùwà dashi

Bidiyo Kalli Miliyan 10 da kayan Abinci, Shinkafa, Kaza, da Talotalo, lemu da za’a kai a matsayin kudin fansa dan kubutar da wani da aka yi Gàrkùwà dashi

Duk Labarai
Bidiyon yanda aka tara Miliyan 10 a matsayin kudin fansa za'a kaiwa 'yan Bindiga ya dauki hankulan mutane sosai a kafafen sada zumunta. Rahoton Bidiyon yace an tara kudinne ta hanyar neman taimako. Sannan 'yan Bindigar sun nemi a kuma kai musu Lemu da kaza da sauran kayan abinci wanda suma sun kai Naira Miliyan 1. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1918310544060170580?t=Gi4pQc0qWeFOsOA26eFvzg&s=19 Mutane dai sun yi ta Allah wadai kan lamarin.
Ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu

Ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu matuka a yayin da suka bayyana yawa kudaden da suka samu a watanni 3 na farkon shekarar nan. A baya dai bankunan kan sau jimullar ribar Naira biliyan 150 a iin wannan lokaci amma da alama lamura sun canja. An alakanta hakan da hauhawar farashin kayan masarufi inda a yanzu bankunan ke kashe kudade da yawa wajan gudanar da ayyukansu fiye da da. Misali bankin GTCO ya samu raguwar riba da kaso 41 cikin 100, shi kuma bankin First Bank ya samu raguwar riba ne da kaso 20.2 cikin 100. Da dai sauransu.
Da Duminsa: Ji Abinda Dan shugaba kasa, Seyi Tinubu yace bayan da shugaban kungiyar daliban Najeriya yace yasa an masa dukan kawo wuka saoda yaki goyon bayan Tinubu

Da Duminsa: Ji Abinda Dan shugaba kasa, Seyi Tinubu yace bayan da shugaban kungiyar daliban Najeriya yace yasa an masa dukan kawo wuka saoda yaki goyon bayan Tinubu

Duk Labarai
A yaune aka tashi da labarin shugaban kungiyar Dalibai ta kasa, Comrade Atiku Abubakar Isah inda ya zargi dan shugaban kasa, Seyi Tinubu da daukar nauyin 'yan daba suka dakeshi. Yace an masa wannan cin zarafine saboda yace ba zai goyi bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba. Saidai a martaninsa, Dan shugaban kasar, Seyi Tinubu yace wannan zargi ba gaskiya bane. A sakon da ya fitar ta shafinsa na Instagram, Seyi Tinubu yace shi baima taba haduwa da shugaban kungiyar dalibanba.
An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC

An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC

Duk Labarai
An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC. Muna rokon gwamnatin jihar Kebbi da ta dubi girman Allah ta saki wannan bawan Allah Muktar da aka kama a yau aka tura gidan yari. Laifin Muktar daya ne, saboda ya yi 'sharing' wani 'posting' wanda wata gidan jarida ta ruwaito na cewa " Gwamnan jihar Kebbi zai bar jam'iyyar APC". Sanadiyyar wannan posting din da wannan bawan Allah ya yi sharing a page dinsa, yau an kama shi an gurfanar da shi kotu. Babu wani jayayya aka wuce da shi gidan yari. Muktar ya fito ya bada hankuri na wannan posting din da ya yi, amma kuma ba'a duba masa ba, saida aka kama shi aka gurfanar da shi a kotu. Mun san Gwamnan jihar Kebbi mai adalci ne, dan Allah ka dubawa wannan bawan Allah. Yana da iyali kuma yana da 'yan u...
Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Gwamnan Katsina ya ba da hutun aiki saboda ziyarar Tinubu

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ya ayyana yau Juma'a a matsayin ranar hutu ga ma'aikata domin "tarɓar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu" da ke ziyara a jihar tasu. Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayin jawabin da ya gabatar a taron Ranar Ma'aikata. "Ina mai farin cikin shaida muku cewa Shugaba Tinubu zai kawo ziyara Katsina gobe [Juma'a] domin buɗe ayyuka da dama da muka kammala cikin shekara biyu da suka wuce," in ji gwamnan. "Saboda haka, na ayyana goben a matsayin ranar hutu saboda ma'aikata su samu damar haɗuwa da mu wajen tarɓar shugaban ƙasa." A jiya Alhamis ne fadar shugaban Najeriya ta sanar cewa Tinubu na jam'iyyar APC zai kai ziyarar aiki ta kwana biyu a jihar da ke arewa maso yamma kuma ta tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Yau juma’a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da Sarki Sanusi II da Sarki Aminu Ado kowa ya naɗa nasa Galadiman

Yau juma’a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da Sarki Sanusi II da Sarki Aminu Ado kowa ya naɗa nasa Galadiman

Duk Labarai
Yau juma'a an shiga ruɗani a birnin Kano kan sanin ainihin Galadiman Kano na gaskiya bayan da masu ikirarin sarautar Kano biyu kowa ya naɗa nasa Galadiman. Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, ya jagoranci majalisarsa da hakimai da magoya bayansa naɗa ɗan uwansa Sunusi Ado Bayero, a matsayin sabon Galadiman Kano. Shima Sarkin Kano Muhammad Sunusi ll ja jagoranci tasa majalisar da hakiman da ke masa biyayya da masoya in da ya naɗa ɗan uwan mahaifinsa wato Munir Sunusi, a matsayin sabon Galadiman Kano. Sarautar Galadiman Kano ta rabu biyu ne tun bayan rasuwar marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi. Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya halarci fadar masarautar Kano da ke Kofar Kudu in da aka Sarki Sunusi ya yi nasa naɗin, yayin da magoya bayan jam'iyyar APC da ke adawa da Gwamnat...
Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Wata Sabuwa: Sanata Natasha Akpoti ta bani Naira Miliyan 200 dan in kalawa Sanata Godswill Akpabio sharri>>Inji Dr. Duru

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Wata farfesa a kasar Amurka me suna Dr. Sandra Duru ta zargi Sanata Natasha Akpoti da nemanta da ta kullawa Sanata Godswill Akpabio sharri tace yana safarar sassan jikin dan Adam. Dr. Sandra Duru ta bayyana hakane a cikin hirar waya data nada da suka yi ita da Sanata Natasha Akpoti. Saidai Sanata Natasha Akpoti tace ita bata ma santa ba, dalili kenan da yasa Dr. Sandra Duru ta mikawa jami'an tsaro hirar da suka yi dan su yi bincike akai. Rahoton yace Sanata Natasha Akpoti ta yi hakanne a yayin da ta ga cewa sharrin da ta ke shirin kullawa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio na cewa ya nemeta da lalata bai yi nasara ba. Matar wadda kuma 'yar jarida ce tace Sanata Natasha Akpoti bata da wata hujja akan zargin da takewa kakakin majalisar.