Sunday, December 14
Shadow
‘Yan Najeriya miliyan 2 ne ke fama da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki: Karanta Jadawalin Jihohin da suka fi yawan masu cutar a Najeriya

‘Yan Najeriya miliyan 2 ne ke fama da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki: Karanta Jadawalin Jihohin da suka fi yawan masu cutar a Najeriya

Duk Labarai
Jihohi 3 ne suka fi yawan masu dauke da cutar Kanjamau me karya garkuwar jiki a Najeriya. Jihohin sune Rivers, Benue, and Akwa Ibom, hakan ya bayyana ne daga hukumar dake kula da cutar ta kasa. Rahoton yace mutane sama da miliyan 2 ne ke fama da cutar a Najeriya. Jihohin dake da yawan mutane masu cutar sune kamar haka: Rivers nada mutane 208,767 Benue na da mutane 202,346 Jihar Akwa Ibom na da mutane 161,597 Jihar Legas na da mutane 108,649 Jihar Anambra na da mutane 100,429 Sai Abuja dake da mutane 83,333 Delta na da mutane (68,170) Imo na da mutane (67,944) Enugu na da mutane (61,028) Edo na da mutane (60,095) Taraba na da mutane (58,460) abia na da mutane (54,655) Kaduna na da mutane (54,458) Kano na da mutane (53,972) Jihar Filato...
Sanata Neda Imasuen na shirin komawa jam’iyyar APC

Sanata Neda Imasuen na shirin komawa jam’iyyar APC

Duk Labarai
Sanata Neda Imasuen daga jihar Edo na shirin komawa jam'iyyar APC daga jam'iyyar Labour Party. Hakan na faruwa ne yayin da ake ganin yana hada alaka me kyau da 'yan APC a jihar ta Edo kamar yanda kafar jaridar Vanguard ta ruwaito. Hakanan Rahoton yace Gwamnan Edo, Monday Okpebholo ya aike da wakilinsa me bashi shawara a harkar siyasa dan ya kara jawo Neda Imasuen ya shiga jam'iyyar sa.
Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar ‘yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu’a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiyar Rashin Lafiya

Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar ‘yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu’a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiyar Rashin Lafiya

Duk Labarai
Bayanan da ke yawo a shafukan sada zumunta na bayyana cewa shahararren mai fafutukar ƙwatar 'yancin bil-adama, wato Ahmad Isah (Ordinary President), yana buƙatar addu'a ta musamman domin yana cikin sarƙaƙiya. Allah Ubangiji ya kawo masa ɗauki na gaggawa.
Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka hàrbè wani dan Daba me suna Halifa Baba a Kano wanda duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun sa a ciki

Kalli Bidiyon yanda ‘yansanda suka hàrbè wani dan Daba me suna Halifa Baba a Kano wanda duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun sa a ciki

Duk Labarai
Rahotanni daga unguwar Gwammaja da ke nan Kano sun bayyana yadda a ka harbi wani rikakken dan daba, Halifa Baba, yayin arangama tsakanin jami'an tsaro da bata-gari a yankin. A na zargin cewa duk wani kwace da fashi da aikata sauran miyagun ayyuka da sa hannun Halifa Baba a ciki. Majiyarmu tace bisa dukkan alamu Halifa Baba rai ya yi halinsa. https://www.tiktok.com/@garkuwanyancrypto/video/7496266492581907717?_t=ZM-8vlrVEM7buw&_r=1 Shaidu sun ce jami'an 'yan sandan Dala Division ne su ka dauke Halifa Baba domin ci gaba da bincike. Daga NasaraRadio
Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Yaro mai shekaru 11 ya mùtù bayan ya fado daga bishiyar mangwaro

Duk Labarai
Wani yaro dan shekara 11 mai suna Joshua Samson ya mutu bayan ya fado daga bishiyar mangwaro a kauyen Bugakwo da ke karamar hukumar Kuje a babban birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin Bugakwo mai suna Danjuma, ya shaidawa DAILY TRUST cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, a lokacin da marigayin ya hau bishiyar mangwaro don ya tsinka. Ya ce yaron ya hau bishiyar mangwaron ne domin ya tsinko mangwaro, amma sai ya zame daga kan reshen ya fado kasa. Ya ce daya daga cikin yaran da suka je diban mangwaron ne ya ruga gida yana kuka ya kai rahoto ga iyayen marigayin, inda suka garzaya da shi asibiti. Ya ce yaron ya mutu ne bayan kansa ya bugu a kan dutse a karkashin bishiyar mangwaron, inda ya ce an binne yaron. “Ma’aikatan lafiya a cibiyar lafiya ta Kwaku sun tabbatar da mutuwarsa s...
Kada ku bai wa ƴansanda bashin da ba za su iya biya ba, IG ya shawarci ƴan Nijeriya

Kada ku bai wa ƴansanda bashin da ba za su iya biya ba, IG ya shawarci ƴan Nijeriya

Duk Labarai
Sufeto Janar na Ƴansanda, Dr. Kayode Egbetokun, ya shawarci al’ummomin da jami’an tsaro ke aiki a yankunan su da su daina ba su rancen manyan kudade waɗanda za su wahala wajen biya. IG ɗin, wanda Kwamishinan ‘Yansanda na Jihar Kogi, Miller Dantawaye, ya wakilta, ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin bikin ƙaddamar da sabuwar hedikwatar ‘yansanda a gundumar Imane, karamar hukumar Olamaboro ta jihar. “Bari in ja kunnen al’ummar yankin cewa yayin da suke mu’amala da jami’an da za a turo musu, wasu daga cikinsu za su nemi taimakon kuɗi da rance, amma kada ku ba su rance mai yawa da za su gagara biya,” in ji Dantawaye. Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su kula da sabon ofishin ‘yan sanda, wanda shine irinsa na farko a yankin, wanda wani ɗan asalin yankin, Dr. Peter Ali, ya gina kum...