Darajar hannun jari da Dala sun sake faduwa a Amurka saboda Trump
Darajar hannun jari a Amurka da kuma kuɗin ƙasar Dala, ta ƙara faɗuwa, bayan da Shugaba Trump ya sake nanata sukar da yake yi wa shugaban babban bankin ƙasar.
A wani saƙo da ya sanya a shafinsa na sada zumunta da muhawara na - Truth Social, Mista Trump ya kira, shugaban bankin Jerome Powell a matsayin babban mai asara, saboda ya ƙi rage yawan kuɗin ruwa.
Wannan matsala da ke ci gaba ta sake tasowa ne a wannan karon yayin da shugabanni da jagororin harkokin kudade suke nufar babban birnin Amurka - Washington domin halartar taron Babban Bankin Duniya, da kuma Asusun Bayar da Lamuni na duniya, IMF.
Shugaban kamfanin zuba jari na kamfanin Scharf Investments, Brian Krawez, ya yi bayani kan wannan hali na kara sulmiyowar darajar hannayen jari na Amurka da kuma darajar Dalar, bayan da Sh...








