Monday, December 15
Shadow
Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman Kiristoci suka soki Gwamnatinsa

Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman Kiristoci suka soki Gwamnatinsa

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da martani bayan da manyan malaman kiristoci, Bishop Matthew Hassan Kukah da Pastor Tunde Bakare suka soki Gwamnatinsa. A sakonsu na bikin Easter, Manyan malaman kiristocin sun nemi shugaban kasar ya dauki matakai akan matsin tattalin arziki da matsalar tsaro da ake fama da ita. Saidai da yake mayar da martani ta bakin kakakinsa, Daniel Bwala, shugaba Tinubu yace a wasu bangare da Fasto Tunde Bakare ya sokeshi sun sha banban amma kuma yana da 'yanci a matsayinsa na dan kasa ya bayyana ra'ayinsa. Yace amma shugaban kasar ya mayar da hankali wajan ganin ya cika alkawuran da ya daukarwa 'yan Najeriya.
Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga ta hanyar karbar kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 14

Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga ta hanyar karbar kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 14

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Bankunan Najeriya sun samu kudin shiga daga kudaden ruwa da suke karba a hannun wadanda suka baiwa bashi da suka kai Naira Tiriliyan 14.26. Hakan ya bayyana ne bayan kammala kididdigar da aka yi ta kudaden shigan bankunan a shekarar 2024. Bankunan da suka samu wadannan kudaden shigar sune, Fidelity, UBA, GT Bank, First Bank, Wema Bank, Stanbic IBTC, FCMB, Access, da Zenith Bank. Rahoton yace a shekarar 2023 bankunan sun samu kudin ruwa da suka kai Naira Tiriliyan 6.49 wanda idan aka hada da kudaden ruwan da suka samu a shekarar 2024 na Tiriliyan 14.26, hakan na nufin sun samu karin kaso 119.55 cikin dari kenan na kudin ruwan. Saidai a gefe guda, yayin da bankunan ke murnar samun kudin ruwa daga hannun wadanda suka baiwa bashin, su kuma wadanda suka k...
Ji yanda ‘Ƴàn bìndìgà ke ci gaba da ɗora wa al’umma haraji a Zamfara

Ji yanda ‘Ƴàn bìndìgà ke ci gaba da ɗora wa al’umma haraji a Zamfara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Zamfara a arewacin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun saka harajin miliyoyin naira ga wasu al'umomi da ke yankin Ɗan Kurmi a ƙaramar hukumar mulki ta Maru. Ƴanbindigar sun ayyana Laraba a matsayin ranar wa'adin biyan kuɗin amma tuni suka fara aiwatar da dokar tsare mutane a garin Zargado har sai an biya kudin a matsayin diyya. Al'ummar yankin da abin ya shafa sun sheda wa BBC cewa sun samu kansu a wannan tasku ne bayan da wasu mazauna yankin suka kona daji da kuma hare-haren da sojoji suka kai wa 'yanbindigan shi ne barayin dajin suka dora musu wannan haraji na naira miliyan 60. Honarabul Iliyasu Salisu Dankurmi ya tabbatar wa da BBC wannan lamari : ''Sojoji sun shigo aiki wannan yanki sun koma to kuma yanzu 'yanbindiga sun zo sun aza mana haraji, suka ce sai ...
Kalli Bidiyon yanda Gobara ta tashi a wajen sayar da Gas a Rijiyar Zaki Kano, Ji yanda Tukwanen Gas suka rika fashewa suna kara kamar Bàm

Kalli Bidiyon yanda Gobara ta tashi a wajen sayar da Gas a Rijiyar Zaki Kano, Ji yanda Tukwanen Gas suka rika fashewa suna kara kamar Bàm

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Kano na cewa an samu fashewar tukunyar gas a wani wajan sayar da gas din dake Dorawar 'yan Kifi, Rijiyar Zaki. A bayanan da hutudole ya samu shine ba'a samu asarar rayuka ko jikkata ba saidai asarar Dukiya. A bidiyon da suka rika yawo a kafafen sada zumunta, an ga da jin yanda tukwanen gas din duka rika fashewa kamar bam na tashi. https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495415482929974583?_t=ZM-8vhcbEDH8TN&_r=1 https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495418146510179639?_t=ZM-8vhcgdjSPDT&_r=1 https://www.tiktok.com/@kingkadoo1/video/7495422464655101189?_t=ZM-8vhcl2xDLao&_r=1 https://www.tiktok.com/@a.k.a.i.s.u/video/7495433889079463174?_t=ZM-8vhcsqiCr3O&_r=1 Saidai daga baya 'yan kwana-kwana sun kai wajan sun kashe gobara...
Kiran mutane su tashi tsaye su kare kansu bashine mafita ba ga matsalar tsaro>>Bulama Bukarti ya mayarwa da T.Y Danjuma Martani bayan da yace mutane su tashi tsaye su kare kansu Gwamnati ba zata iya ba ita kadai

Kiran mutane su tashi tsaye su kare kansu bashine mafita ba ga matsalar tsaro>>Bulama Bukarti ya mayarwa da T.Y Danjuma Martani bayan da yace mutane su tashi tsaye su kare kansu Gwamnati ba zata iya ba ita kadai

Duk Labarai
Babban me sharhi akan Al'amuran tsaro, Bulama Bukarti ya mayarwa da Tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma martani kan kiran da yayi mutane su tashi tsaye su kare kansu game da matsalar tsaro. T.Y Danjuma yace gwamnati ba zata iya ba ita kadai inda yace kamata yayi mutane su tashi su kare kansu. Saidai a hirar da aka yi dashi a Channels TV, Bulama Bukarti ya bayyana cewa wannan ba mafita bace. Yace idan aka yi hakan, makamai zasu karu a hannun farar hula wanda hakan zai kawo ci gaba da kisan mutane ba tare da hukunci ba.
2027: Nan da watanni 6 yankin Arewacin Najeriya zai bayyana matsayar sa kan zaben shugaban kasa – Hakeem Baba-Ahmed

2027: Nan da watanni 6 yankin Arewacin Najeriya zai bayyana matsayar sa kan zaben shugaban kasa – Hakeem Baba-Ahmed

Duk Labarai
2027: Nan da watanni 6 yankin Arewacin Najeriya zai bayyana matsayar sa kan zaben shugaban kasa - Hakeem Baba-Ahmed. Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai bai wa Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima shawara kan harkokin siyasa, ya yi gargadin cewa Arewacin Najeriya na iya daukar matsaya mai tsauri dangane da makomar siyasar yankin idan aka ci gaba da watsi da koke-koken yankin. A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Baba-Ahmed ya bukaci ‘yan Arewa da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya tare da lura da "makaryata" da ke aiki don raunana yankin. “Arewacin Najeriya za ta tsaya ta kare kanta, wallahi,” in ji shi. “Ya kamata Arewa ta yi hattara sosai, ta guji ‘yan siyasa na cin amana da kuma duk wani abu da zai kawo rabuwar kai.” Ya jaddada bukatar h...
Da Duminsa: Cikin darennan Bàm ya fashe a gidan yarin Maiduguri jihar Borno

Da Duminsa: Cikin darennan Bàm ya fashe a gidan yarin Maiduguri jihar Borno

Duk Labarai
Rahotanni daga Maiduguri na cewa wani abin fashewa me kama da bam ya fashe a gidan yarin dake garin da daren Ranar Lahadi. Lamarin ya farune da misalin karfe 9 na darennan inda hakan yayi sanadiyyar tashin wuta a dakin da ake tsare da Charles Okah. Wasu shaidu sun ce an cilla wani abu me kama da bam a dakin da ake tsare da Charles Okah din inda aka ga hayaki na tashi. Wannan lamari ya biyo bayan budaddiyar wasikar da Charles Okah ya aikewa ministan harkokin cikin gida, Olubunmi-Ojo ne inda yake korafi kan yawaitar cin hanci a gidajen yarin Maidugurin. Rahoton na Sahara reporters yace Okah ya rika tari inda aka ji yana fadin an cilla masa bom a dakinsa. Saidai babu wanda ya kai masa dauki dan kuwa a cewar rahoton ma'aikatan gidan yarin dake aikin dare basa nan. Hakanan wan...
Taliya Ba Za Ta Yi Tasiri Ba A Zaɓen 2027 Saboda Kan Mage Ya Waye, Cewar Sanata Babba Kaita

Taliya Ba Za Ta Yi Tasiri Ba A Zaɓen 2027 Saboda Kan Mage Ya Waye, Cewar Sanata Babba Kaita

Duk Labarai
Taliya Ba Za Ta Yi Tasiri Ba A Zaɓen 2027 Saboda Kan Mage Ya Waye, Cewar Sanata Babba Kaita. Wayewa a siyasa ita ce damawa da kowa ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ko yankin da mutum ya fito ba, don haka ya zama wajibi a dama da dukannin bangarorin ƙasar nan muddin ana yin siyasa ne don cigaban al’umma. Yin wani abu akasin haka kuskure ne babba a siyasance, domin mutane ba su da mantuwa. Komai daren daɗewa za su rama abin da aka yi musu idan lokacin yin ramuwar ya zo. Duk da cewa mutane na cikin yunwa da fatara, a wannan karon Taliyarka ba za ta yi ma amfanin komai ba saboda kan mage ya waye! Daga Jamilu Dabawa
Kalli Bidiyon hudubar da uba yawa diyarsa bayan daurin aure da ta dauki hankula sosai

Kalli Bidiyon hudubar da uba yawa diyarsa bayan daurin aure da ta dauki hankula sosai

Duk Labarai
Wani mahaifi bafulatani ya dauki hankulan mutane sosai musamman a kafafen sadarwa bayan da aka ga irin hudubar da yawa diyarsa da aka daurawa aure. Bidiyon hudubar ya watsu sosai a kafafen sadarwa inda ake ya sanya masa Albarka. Ya gargadi diyarsa kada ta sake ta saurari kowa idan ba mijinta ba. https://www.tiktok.com/@fulani_tutor/video/7232318925684460805?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7232318925684460805&source=h5_m&timestamp=1745185435&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7483198445273974549&am...
Atiku ya nemi Peter Obi ya zama mataimakinsa a 2027 dan su kwace mulki a hannun Tinubu, inda shi kuma yayi Alkawarin yin mulki sau daya ya sauka ya barwa Peter Obin

Atiku ya nemi Peter Obi ya zama mataimakinsa a 2027 dan su kwace mulki a hannun Tinubu, inda shi kuma yayi Alkawarin yin mulki sau daya ya sauka ya barwa Peter Obin

Duk Labarai
Rahotanni daga bangaren Atiku na cewa jiga-jigai sun nemi hada kai da Peter Obi ganin yana da mabiya sosai musamman a kudancin Najeriya. Rahoton yace an nemi goyon bayan Peter Obi dan ya zama mataimakinsa a shekarar 2027 dan su kwace mulki daga hannun shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Rahoton yace bangaren Atiku sun yi Alkawurin yin mulki sau daya inda a shekarar 2031, za'a barwa Peter Obi shi kuma yayi takarar shugaban kasa. Saidai bangaren Peter Obi sun ki amincewa inda suka ce ai kudu bata kammala wa'adinta na zango biyu ba kamar yanda Buhari yayi. Dan haka suka ce idan ba Peter Obi bane zai zama ahugaban kasa ba, to basu yadda ba. Saidai ana ganin har yanzu wannan tattaunawa bata kare ba inda ake tsammanin zata iya cimma gaci.