Monday, April 6
Shadow
Ma’aikatan Shari’a zasu tsunduma yajin aikin sai mama ta gani gobe, Litinin

Ma’aikatan Shari’a zasu tsunduma yajin aikin sai mama ta gani gobe, Litinin

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Ma'aikatan shari'a na Najeriya karkashin Kungiyarsu ta (JUSUN) sun nace akan tafiya yajin aiki gobe, Litinin, 2 ga watan Mayu. Ma'aikatan bangaren babbar kotun tarayya ne zasu tafi yajin aikin inda bangaren kotun Koli suka fasa shiga yajinnaikin. Wata majiya tace shugaban hukumar DSS ya zauna da ma'aikatan tsawon awanni 4 amma duk da haka sun ce ba zasu fasa tafiya wannan yajin aikin ba. Sakataren kungiyar, Comrade Mohammed Isah yace zasu fara yajin aikin gobe Litinin inda yace yana kiran duka ma'aikatansu da su zauna a gida kada su je wajan aiki. Saidai yace a goben ma akwai wani zama sa za'a sake yi.
Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ya jefa Mutanen Najeriya cikin matsanancin Talauci>>Inji Janar Buratai

Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ya jefa Mutanen Najeriya cikin matsanancin Talauci>>Inji Janar Buratai

Duk Labarai
Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jefa 'yan Najeriya cikin matsin talauci. Ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwar tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi. Yace gwamnatocin baya a hankali suka rika jefa 'yan Najeriya cikin talauci amma Gwamnatin Tinubu, Lokaci guda ta jefa mutane saboda tsare-tsaren ta data gudanar masu tsauri. Saidai yayi fatan nan da shekaru biyu masu zuwa a samu saukin rayuwa wanda yace idan ba haka ba, akwai matsala.
Kasar Ìran ta Kàshè wani munafiki dan kasarta dakewa Kasar Israyla leken Asiri tana biyanshi kudi

Kasar Ìran ta Kàshè wani munafiki dan kasarta dakewa Kasar Israyla leken Asiri tana biyanshi kudi

Duk Labarai
Kasar Iran ta kàshè wani dan kasarta me suna Pedram Madani dan kimanin shekaru 41 wanda ijiniya ne saboda samunsa da laifin yiwa kasar Israyla leken Asiri a Iran din. An kashe shine ta hanyar Rataya bayan samunsa da laifin haduwa da wakilan kungiyar leken Asirin kasar Israela ta Mossad da karbar kudi yana musu aiki. An ratayeshine ranar 28 ga watan Mayu a gidan yarin Ghezelhesar Prison, Karaj. Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi Allah wadai da lamarin.
Jihar Ekiti ta Haramta Shan Tàbà

Jihar Ekiti ta Haramta Shan Tàbà

Duk Labarai
Jihar Ekiti, ta haramta shan Taba a babban birnin jihar, Ado Ekiti. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr. Felani Oyebanji ne ya bayyana hakan a wajan zagayowar ranar yaki da shan taba ta Duniya a birnin Ado Ekiti. Yace illar da taba kewa lafiyar dan adam ce tasa suka dauki wannan mataki. A wani labari me kama da wannan ma, kasar Faransa ma na shirin haramta shan taba sigari.
Da Duminsa: Mutane 9 sun mùtù bayan fashewar Bam a wata tashar mota dake jihar Borno

Da Duminsa: Mutane 9 sun mùtù bayan fashewar Bam a wata tashar mota dake jihar Borno

Duk Labarai
Rahotannin da hutudole ke samu na cewa a kalla mutane 9 ne suka mutu wasu suka jikkata bayan fashewar bam a tashar motar dake Maimalari a karamar hukumar Guzamala dake jihar Borno. Rahoton yace an dasa bam dinne a tashar motar wnda daga baya ya tashi. Lamarin ya farune da misalin karfe 11 a.m. na safiyar ranar Asabar. Jaridar Punchng ta ruwaito kakakin majalisar jihar Borno, Hon. Abdulkarim Lawan ya tabbatar mata da faruwar lamarin. Ya mika ta'aziyya ga iyalan mamatan inda yayi fatan samun sauki ga wadanda ke kwance a Asibiti. Ya koka da yawaitar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin Jìhàdì.
Murnar cin kofin Championships League din PSG yasa mutane 2 sun mùtù dan sanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai a birnin Paris na kasar Faransa, an yi kòne-kòne da sace-sace

Murnar cin kofin Championships League din PSG yasa mutane 2 sun mùtù dan sanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai a birnin Paris na kasar Faransa, an yi kòne-kòne da sace-sace

Duk Labarai
Rahotanni daga birnin Paris na kasar Faransa na cewa an yi kone'kone da sace sace da lalata dukiya a yayin da ake murnar cin kofin Championships League da kungiyar PSG ta yi. Rahotannin sun kuma ce an kashe mutane 2 yayin murnar sannan an kama sama da 500 da suka aikata laifuka. https://twitter.com/Megatron_ron/status/1928945703352410317?t=2ftRc57m_y3NgxI415Ud6g&s=19 Hakanan rahoton yace dansanda daya na can rai kwakwai mutu kwakwai saboda lamarin. https://twitter.com/MegaGeopolitics/status/1929118696674361514?t=aMRoiiBdqoj7G4li9UZaXQ&s=19 'Yansanda sun fito da barkonon tsohuwa dan magance wannan matsala ta hatsaniya data kaure.
Gaba da gaba na faɗa wa Tinubu ba zan goya masa baya ba – Amaechi

Gaba da gaba na faɗa wa Tinubu ba zan goya masa baya ba – Amaechi

Duk Labarai
Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon fara gangamin yaƙin neman zaɓen 2023 ne ya yanke shawarar ba zai zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba, inda ya ce sun haɗu gaba da gaba, kuma ya faɗa a take cewa shi ba zai zaɓe shi ba. Amaechi ya ce hakan ya sa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa na ƙin taimakon yaƙin zaɓen Tinubu, saboda a cewarsa ya gano tun da wuri cewa aikin zai yi wa shugaban nauyi na mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Amaechi ya bayyana haka ne a wajen taron murnar cikarsa shekara 60 a duniya wanda aka yi jiya Asabar a Abuja. "A Yola muka haɗu da Tinubu, inda na faɗa masa cewa ni ba zan goya masa baya ba. Kuma ban yi ba, kuma ban zaɓe shi ba. Magana ce ta tunanin ba zai iya ba. "Wasu daga cikinmu da suke na...