Mun kusa fara biyan alawus ɗin naira 77,000 – NYSC
Hukumar NYSC ta ce ta kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus ɗin naira 77,000.
Hukumar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rashin fara biyan sabon alawus ɗin bayan an sanar da ƙari daga naira 33,000 da ake biya biyo bayan ƙara mafi ƙanƙantar albashi.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin fara biyan sabon alawus ɗin, amma har yanzu ba a fara biya ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga masu bautar ƙasar.
A watan Janairu, darakta-janar na NYSC, Birgediya-janar Yushau Ahmed ya sanar da cewa daga watan Fabrairu za a fara biyan sabon alawus ɗin, amma kuma ba a biya ba a watan na Fabrairu da ya gabata.
Daraktan riƙo na hulɗa da jama'a na hukumar, Caroline Embu, ta ce suna jiran kuɗi ne da umarni kafin fara biyan sa...








