Monday, December 15
Shadow
Ku yiwa Najeriya addu’a, Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta gayawa musulmai da suka fara Azumin watan Ramadana

Ku yiwa Najeriya addu’a, Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta gayawa musulmai da suka fara Azumin watan Ramadana

Duk Labarai
Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta nemi 'yan Najeriya musulmai da su yi amfani da watan Ramadana wajan nuna son kasa da yiwa kasar addu'a. Remi ta fitar da wannan sanarwa ne ranar Juma'a a babban birnin tarayya, Abuja a yayin da Musulmai ke shirye-shieryen fara azumin watan Ramadana. Ta yi fatan watan na Ramadana zai kawo zaman lafiya, jin dadi da cikar burin rayuwa ga iyalan musulman kasarnan.
Mijina ba Dan iska bane, Sharri kika masa, Matar Sanata Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu inda tace sai ta biya diyyar Naira Biliyan 250 na bata sunan data taiwa mijinta

Mijina ba Dan iska bane, Sharri kika masa, Matar Sanata Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu inda tace sai ta biya diyyar Naira Biliyan 250 na bata sunan data taiwa mijinta

Duk Labarai
Matar kakakin majalisar Dattijai, Unoma Akpabio ta maka Sanata Natasha Akpoti a kotu bisa zargin bata suna da take hakkin bil'adama. Ta kai Sanata Natasha Akpoti babbar kotun tarayyane dake Abuja. Hakan ya biyo bayan zargin da sanata Natasha Akpoti tawa Akpabio na cewa ta fara samun matsala a majalisar ne tun bayan da ta ki yadda ta yi lalata da da sanata Akpabio. Matar sanata Akpabio ta bayyana cewa, zargin da Sanata Natasha Akpoti tawa mijinta yasa ita da 'ya'yanta sun shiga firgici da kuma tsoron za'a iya kai musu harin da zai iya sawa su rasa rayuwarsu. Dan haka matar Akpabio ta nemi kotun da ta ayyana maganar da Sanata Natasha Akpoti ta yi a matsayin take hakkin mutuncin mijinta. Sannan ta nemi kotun data tursasa Sanata Natasha Akpoti ta biya diyyar Naira Biliyan 250 a...
Reno Omokri ya caccaki ‘yan Kudu masu zagin jihar Bauchi saboda ta bada hutun watan Ramadana, yace jihohin da ake kulle makarantu duk ranar Litinin ya kamata a caccaka ba jihar Bauchi ba

Reno Omokri ya caccaki ‘yan Kudu masu zagin jihar Bauchi saboda ta bada hutun watan Ramadana, yace jihohin da ake kulle makarantu duk ranar Litinin ya kamata a caccaka ba jihar Bauchi ba

Duk Labarai
Tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya caccaki 'yan uwansa 'yan kudu da suke zagin jihar Bauchi saboda ta bayar da hutun Azumin watan Ramadana ga makarantu. Omokri ya bayyana cewa fiye da sau 10 yana ziyarar jihar Bauchi. Yace yana son jihar Bauchi kuma mutanenta wayayyu ne wanda sun san abinda suke so a rayuwa. Sannan yace mutanen Bauchi sun zabi gwamnansu kuma suna goyon bayansa a kan duk wani abu da yayi. Yace kuma a Dimokradiyya ake kuma mutanen Bauchi suna goyon bayan abinda gwamnatinsu ta yi na bayar da hutun watan Ramadana, dan haka bai kamata wani ya zauna a Legas, ko Fatakwal ko Anambra ya rika jin haushin wannan mataki ba. Yace jihar Bauchi ba cima zaune bace a Najeriya, jihace wadda take bayar da gudummawa sosai wajan ci gaban Najeriya musamman ta bangaren a...
Wasu Kiristoci Musamman daga kudancin Najeriya na yiwa Jihohin da suka bayar da hutun Ramadan Dariya

Wasu Kiristoci Musamman daga kudancin Najeriya na yiwa Jihohin da suka bayar da hutun Ramadan Dariya

Duk Labarai
Wasu Kiristoci Musamman daga kudancin Najeriya na yiwa jihohin musulmai da suka bayar da hutun watan Ramadana Dariya. A ganinsu, wannan hutu koma bayane ga ci gaban kasa. Bayan wallafa labaran da kafafen watsa labaran Najeriya suka yi, an samu wasu na bayyana ra'ayoyi kamar haka: Wani me suna King Premier ya bayyana cewa suna Bankuna ya kamata a rufesu, ba makarantu kadai ba. Shima wani me suna AlleZamani ya tambaya cewa shin zuwan Ramadan yasa an kulle makarantu a kasar Saudi Arabia? Inda ya kara da cewa ina zaune da sakarkarun mutane a kasa daya. Binciken da Shafin Hutudole yayi ya gano cewa, a kasar Saudiyya ba'a kulle makarantu ba amma an rage lokutan karatune saboda zuwan watan Ramadan. Wani me sunan Nigeria Exchange rate yace nan gaba kuma irin wadannan jih...
Kungiyoyin Arsenal, Man City, West Ham, Leicester, Man United, Bybit, Kasar Amurka, Real Madrid, Jami’ar Oxford da sauransu sun taya Musulmai murnar shiga watan Ramadana

Kungiyoyin Arsenal, Man City, West Ham, Leicester, Man United, Bybit, Kasar Amurka, Real Madrid, Jami’ar Oxford da sauransu sun taya Musulmai murnar shiga watan Ramadana

Duk Labarai
A yayin da aka shiga watan Ramadana inda a yau muke daya ga wata, Kungiyoyin Kwallon kafa da Gwamnatocin Duniya da makarantu sun taya Musulmai shiga watan na Ramadana. Kungiyar Inter Milan ta kasar Italiya na daga cikinsu: Nottingham Forest ma ta taya musulmai shiga Ramadan: Sakataren majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ma ya taya musulmai murnar shiga Ramadana: Mesut Ozil tsohon dan kwallon Real Madrid da Arsenal ya taya musulmai murnar shiga Ramadan. IItama kungiyar Kwallon kafa ta Juventus ta taya musulmai shiga watan na Ramadana. Kungiyar Real Madrid ma ta taya musulmai murnar shiga watan na Ramadana. Itama Mataimakiyar Sakataren majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Muhammad ta taya musulmai shiga watan Ramadana. Ofishin Jakadan...
Kalli Hotuna: Rahama Sadau ta saki Hotunan Murnar zuwan watan Ramadan

Kalli Hotuna: Rahama Sadau ta saki Hotunan Murnar zuwan watan Ramadan

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau kenan a wadannan hotunan nata data saka a shafinta na sada zumunta tanawa masoyanta barka da zuwan watan Ramadana.
Jihohin Katsina da Bauchi sun bayar da hutun Azumin Watan Ramadan ga ‘yan makaranta

Jihohin Katsina da Bauchi sun bayar da hutun Azumin Watan Ramadan ga ‘yan makaranta

Duk Labarai
Jihohin Bauchi da Katsina sun bayar da hutun Watan Azumin Ramadana ga 'yan makaranta. A jihar katsina, bayan kulle makarantun Gwamnati, Hukumar HISBAH ta jihar ta kuma fitar da sanarwa ga masu marantu masu zaman kansu dasu kulle makarantun nasu har sai bayan Azumin watan Ramadana. Kwamandan HISBAH na jihar, Aminu Usman ne ya fitar da sanarwar inda yace rashin yiwa wannan doka biyayya zai sa a hukunta duk makarantar da aka kama suna karatu. Hakanan a jihar Bauchi na, mahukuntan jihar sun bayar da hutu daga ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa ranar 5 ga watan Afrilu ga makarantu.
Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025

Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025

Duk Labarai
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar na 2025 da ya kama naira tiriliyan 54.99 Kasafin kuɗin na wannan shekara ya zarta na shekarar da ta gabata - wanda aka yi a kan naira tiriliyan 27.5 - da kashi 99.96 cikin 100. Shugaban ya sanya hannu kan kasafin ranar Juma'a a fadarsa da ke Abuja. An dai ƙara yawan kasafin na farko da shugaan ya aikewa majalisa na naira tiriliyan 49.7. A ranar 13 ga watan Fabrairun da muke ciki ne majalisar dokokin ƙasar ta amince da kasafin, bayan muhawara a kansa. An dai tsara kashe naira tiriliyan 14.32 wajen biyan bashi, inda manyan ayyuka za su laƙume naira tiriliyan 23.96.
Ya kamata a binciki Sanata Akpabio kan zargin làlàtà da Natasha Akpoti tai masa>>Inji Atiku

Ya kamata a binciki Sanata Akpabio kan zargin làlàtà da Natasha Akpoti tai masa>>Inji Atiku

Duk Labarai
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yayi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da shugabancin majalisar dattijai da cewa ya kamata au binciki kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio kan zargin da Sanata Natasha Akpoti tai masa na son yin lalata da ita. Atiku a sanarwar da ya fitar ya nemi cewa a matsayin Akpabio na mutum na 3 wanda yafi karfin fada aji a Najeriya, ya kamata ace yana da mutunci da tsare kai da tarbiyya. Atiku yace ya kamata a kafa kwamiti na musamman me zaman kansa da zai binciki sanata Akpabio kan wannan zargi. Atiku yace wannan lamari zai sa Duniya ta fahimci irin tsarin Adalci da Najeriya ke da shi.
Yanda Sanata Akpabio Ya taba rike hannuna a gaban mijina>>Sanata Natasha Akpoti

Yanda Sanata Akpabio Ya taba rike hannuna a gaban mijina>>Sanata Natasha Akpoti

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi ta bayar da labarin yanda Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya taba rike hannunta a gaban mijinta. Tace a lokacin sun je taya Akpabio murnar zagayowar ranar haihuwarsa ne inda mijinta ya rakata. Tace Sanata Akpabio ya kama hannunta ya jata ya rika nuna mata gidansa yayin da mijinta ke binsu a baya. Tace abin ya damu mijinta a lokacin wanda daga nan ya rika cewa ba zata rika yin tafiya ita kadai ba.