Gaba da gaba na faɗa wa Tinubu ba zan goya masa baya ba – Amaechi
Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon fara gangamin yaƙin neman zaɓen 2023 ne ya yanke shawarar ba zai zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba, inda ya ce sun haɗu gaba da gaba, kuma ya faɗa a take cewa shi ba zai zaɓe shi ba.
Amaechi ya ce hakan ya sa ya cika alƙawarin da ya ɗaukar wa kansa na ƙin taimakon yaƙin zaɓen Tinubu, saboda a cewarsa ya gano tun da wuri cewa aikin zai yi wa shugaban nauyi na mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Amaechi ya bayyana haka ne a wajen taron murnar cikarsa shekara 60 a duniya wanda aka yi jiya Asabar a Abuja.
"A Yola muka haɗu da Tinubu, inda na faɗa masa cewa ni ba zan goya masa baya ba. Kuma ban yi ba, kuma ban zaɓe shi ba. Magana ce ta tunanin ba zai iya ba.
"Wasu daga cikinmu da suke na...








