Thursday, July 16
Shadow
Tuni ƴan Najeriya su ka dawo daga rakiyar ɓangaren shari’a – El-Rufai

Tuni ƴan Najeriya su ka dawo daga rakiyar ɓangaren shari’a – El-Rufai

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce mutane da dama a Najeriya sun daina yarda da bangaren shari’a wajen samun adalci. Mista El-Rufai ya kuma zargi bangaren shari’ar da cin hanci da rashawa, yana cewa wasu alkalai da lauyoyi sun sauka daga abinda ke kansu ta hanyar karkata ko karɓar rashawa wajen yanke hukunci. Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin makon shari’a na kungiyar lauyoyi ta Najeriya (Nigerian Bar Association), reshen Bwari, da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin. Ya bayyana cewa rashin amincewar jama’a ga shari’a na da nasaba da yawan jinkiri wajen yanke hukunci da kuma shawarwarin da ake ganin sun samo asali daga son rai ko tasirin wasu masu hannu da shuni a waje. “A gefe guda, bangaren shari’armu—wanda ya kamata ya zama ginshikin adalci —yana fuskan...
Sabon Shèkàu ya fito tare da barazana ga CDS, sojoji da malaman addini

Sabon Shèkàu ya fito tare da barazana ga CDS, sojoji da malaman addini

Duk Labarai
Wani kwamandan Boko Haram da ya kira kansa da cewa shi ne sabon “Shekau,” ya yi barazana ga babban hafsan hafsoshin Najeriya, CDS, Christopher Musa, da malaman addinin Musulunci, da jami’an tsaro, da kuma al’ummomin da ke goyon bayan ayyukan gwamnati na yaki da ta’addanci. Barazanar ɗan ta’addan ba ta rasa nasaba ga gargadin da Musa ya yi tun farko a cikin harshen Hausa, inda ya yi kira ga yan ta’addan da su mika wuya ko kuma su fuskanci fushin sojojin Najeriya. A wani sabon faifan bidiyo da kafar yada labarai ta PRNigeria ta samu kuma ta fassara daga Hausa zuwa turanci, maharin ya mika sakon ban tsoro ga Janar Musa, inda ya bukaci shi da rundunar sojojin Najeriya da su yi watsi da yakin da suke yi da kungiyar. Ya yi ikirarin cewa, kamar magabatan sa, Musa ba zai yi nasarar murkus...
Majalisar Wakilai ta umarci a bada tsaro na tsawon shekaru 10 ga ɗan jaridar da ya bankado badakalar digiri dan kwatano

Majalisar Wakilai ta umarci a bada tsaro na tsawon shekaru 10 ga ɗan jaridar da ya bankado badakalar digiri dan kwatano

Duk Labarai
Majalisar Wakilai ta amince da bada kariya ta tsaro na tsawon shekaru 10 ga wakilin DAILY NIGERIAN mai binciken ƙwaƙwaf, Umar Audu, biyo bayan fallasa yadda ake baƙalar kwali digiri a Kwatano, amhuriyar Benin. Binciken da Audu ya yi a boye ya bankado wani gungun mutane da ke taimaka wa ‘yan Najeriya siyan kwallon digiri da ba su yi karatun ba, wadanda da yawa aka sahale musu aiki a ma'aikatun gwamnati, ciki har da ma’aikatar ilimi suka wanke su ta hanyar damfara. A halin yanzu dai kwamitin majalisar tarayya mai kula da jami’o’i, da fasaha, da harkokin cikin gida, da harkokin kasashen waje, da kuma ci gaban matasa, na binciken badakalar. A zaman sa a yau Litinin, shugaban kwamitin, Abubakar Fulata, ya sanar da umarnin majalisar tare da yin kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da s...
Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, ta janye dakatarwar da ta yi daga haska wasu finafinai 22 a jihar

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, ta janye dakatarwar da ta yi daga haska wasu finafinai 22 a jihar

Duk Labarai
Freedom Radio ta rawaito cewa hukumar tamince da ci gaba da haska fina-finan da ta dakatar a masana'antar Kannywood domin kada masu samar da su, su tafka asara. A wata sanarwa da kungiyar masu shirya fina-finai ta jihar Kano MOPPAN karkashin shugabanta Ado Ahmad gidan Dabino ta fitar ta ce sun yi zama da shugabannin hukumar tace fina finan ta jihar Kano. Sanarwar ta ruwaito cewa, matsayar da aka cimma ta hada da ci gaba da haska fina finan da aka dakatar, tare da bayar da wa'adin mako guda ga masu shirya fina finan su mika duk wani shirin su a gaban hukumar domin tantancewa.
Ina Kira Ga Gwamnati Da Ta Taimaka Ta Dauki Nauyin Ciyar Da Ni Ko Na Tsawon Shekara Daya Ne, Domin Ina Cikin Halin Rayuwa, Saboda Yanzu Ba Na Koshi Kamar A Baya Da Zan Iya Shan Bokiti Uku Na Kunu, Ko Yau Na Ci Masar Dubu Tara Amma Ban Koshi Ba, Jiya Ma Tuwon Dubu Goma Na Ci Amma Sai Maleji Na Yi, Inji Babba

Hukumar EFCC Ta Miƙa Rukunin Gidajen Alfarma 750 Da Ta Kwace A Hannun Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefele Ga Ma’aikatar Gidaje Da Raya Birane Domin Sayar Da Su Ga Ƴan Najeriya, Yau Talata

Hukumar EFCC Ta Miƙa Rukunin Gidajen Alfarma 750 Da Ta Kwace A Hannun Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Emefele Ga Ma'aikatar Gidaje Da Raya Birane Domin Sayar Da Su Ga Ƴan Najeriya, Yau Talata EFCC ta danƙa gidaje 753 da ta ƙwace a hannun Emefiele ga gwamnatin taraiya Hukumar Yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta mika wani gidaje 753 da ke da alaka da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN ga ma’aikatar gidaje da raya birane ta taraiya. Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ne ya mika takardun rukunin gidajen ga Ministan gidaje da raya birane, Ahmed Dangiwa a yau Talata. Rukunin gidajen, wanda ba a kammala ginin su ba, na cikin gundumar Lokogoma na babban birnin tarayya Abuja. A wata sanarwa da Dangiwa ya fitar ta ce shugaba Bola Tinubu ya bayar da ...
Kalli Bidiyon: Kungiyar ‘yan Kwallo na mata na Chelsea suma suna chashewa da wakar Shake Body ta Skales

Kalli Bidiyon: Kungiyar ‘yan Kwallo na mata na Chelsea suma suna chashewa da wakar Shake Body ta Skales

Duk Labarai
Bayan Lamine Yamal na Barcelona ya hau kan wakar Shake body ta mawakin Najeriya Skales, Wakar ta watsu sosai a Duniya. A bayabayannan, Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Chelsea suma sun Chashe da wanann waka a dakin canja kaya. https://twitter.com/ChelseaFCW/status/1924415423425954121?t=fnfZmAw6UeSKouiHS0GXxA&s=19 Wakar dai ta samu an saurareta sau 324k a Spotify
Yanda Mutanen Karkara suka fi na Birni zuwa aikin Hajjijn bana ya kawo cece-kuce

Yanda Mutanen Karkara suka fi na Birni zuwa aikin Hajjijn bana ya kawo cece-kuce

Duk Labarai
Hajjin Bana ya zo da sabon salo a Najeriya inda mafi yawan wadanda ake gani na zuwa Mutanen karkara ne. Hakan ya dauki hankula musamman ganin yanda zuwan Hajjin banan yayi tsada inda mutanen Birni da yawa basa iya biya. Wasu dai na alakanta lamarin da cewa mutanen kauye akwai Noma da kiwo a yayin da wasu kuma ke zargin wasu na amfani da kudaden garkuwa da mutanene. A hajjin na bana dai an kama 'yan Bindiga da suke shirin zuwa aikin Hajji a Abuja da Sokoto wanda hakan ya saka shakku a zukatan mutane.