Shugaban Kasa Tinubu Ya Nada Sabon Jagorancin Hukumar Kula Da Ayyukan Yan Sanda
Shugaba Bola Tinubu ya amince da nadin DIG Hashimu Argungu (Mai Ritaya) a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
Shugaban ya kuma amince da nadin Cif Onyemuche Nnamani a matsayin Sakatare da DIG Taiwo Lakanu (mai ritaya) a matsayin mamba a hukumar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya maye gurbin Solomon Arase a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda (PSC).
Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar, shi ne wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya ce DIG Hashimu Argungu (Mai ritaya) ne sabon shugaban hukumar.
Majalisar dattawa za ta tabbatar da nadin.
Za a nada sauran mambobin hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda a kan lokaci, inji Ngelale.
Bugu da kari, shugaban kasar ya amince da nadin Mr. Mohammed Sheidu a matsayin...






