Saturday, December 20
Shadow
Yanzu-Yanzu:EFCC ta kafa kwamiti dan binciken tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Yanzu-Yanzu:EFCC ta kafa kwamiti dan binciken tsohon gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Kaduna, Siyasa
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kafa wani kwamiti na musamman dan binciken zargin da akewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kan satar Naira Biliyan 423. Za'a binciki tsohon gwamnan ne tare da wasu manyan da suka yi aiki tare da shi a gwamnatinsa. Nan gaba kadan ake sa ran EFCC din zasu gayyaci El-Rufai dan binciken sa. Hukumar ta EFCC tace sun karbi korafi dake bukatar a bincike tsohon gwamnan na jihar Kaduna. za a bincike gwamnan ne tare da sauran mukarrabansa da suka yi aiki tare dashi tsakanin shekarau takwas daya yi akan karagar mulki. Cikin wadanda za a bincika hadda ma'aikatan KADRIS KADRA amma banda injiniya Amina jafar Ladan wadda aikin wata daya kacal tayi.
Da Ɗuminsa: Ba Za Mu Tafi Yajin aiki ba – NLC ta bayyana

Da Ɗuminsa: Ba Za Mu Tafi Yajin aiki ba – NLC ta bayyana

Siyasa
Shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero, ya bayyana cewa kungiyoyin kwadago ba za su tafi yajin aiki a ranar Talata ba, dangane da sabon takaddamar mafi karancin albashi da gwamnati ke fuskanta. Da yake bayar da dalilin daukar matakin, Ajaero ya ce har yanzu ma’aikata ba za su tafi yajin aikin ba saboda a halin yanzu alkaluman na kan teburin shugaban kasa Bola Tinubu kuma ana sa ran za a mayar da martani. Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito shugaban NLC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a ranar Litinin a taron kungiyar kwadago ta duniya da ke gudana a birnin Geneva na kasar Switzerland. Yayin da yake buga misalan gwamnatocin da suka gabata, Ajaero ya ce har yanzu akwai yuwuwar Shugaban kasa ya kara adadin da ake so a gabansa. Sai dai ya yi kira ga Gw...
Hajj 2024: Sarkin Saudiyya ya gayyaci ƴan Najeriya 30 a matsayin baki

Hajj 2024: Sarkin Saudiyya ya gayyaci ƴan Najeriya 30 a matsayin baki

Hajjin Bana
Hajj 2024: Sarkin Saudiyya ya gayyaci ƴan Najeriya 30 a matsayin baki Sarkin Saudiyya Salman Bin Abdulaziz Al Saud, mai kula da Masallatan Harami guda biyu, ya gayyaci 'yan Najeriya 30 a matsayin baki domin halartar aikin hajjin 2024. Gayyatar dai ta ta’allaka ne kan irin gudunmawar da mutanen suka bayar wajen fadada ilimin addinin Musulunci da fadakarwa da ake yi a duk shekara yayin ziyarar aikin Hajji a kasar Saudiyya. Daga cikin ‘yan Najeriya da aka gayyata akwai kwararre kan harkokin kudi da haraji, Dokta Awa Ibraheem, Grand Khadi na Jihar Kwara, Mai Shari’a Abdullateef Kamaldeen, Grand Khadi mai ritaya, Mai Shari’a Idris Haroun, malamin addinin Musulunci na Jihar Legas, Sheikh Imran Eleha, Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa da Hadiza Ndamadi da Sarauniya Seidat Almubarak, matar D...
Ko Kudin Asusun Gwamnatin Kano Kwankwaso Ya Wawushe Baki Daya, Mu Kanawa Mun Yafe Masa, Inji Aisha Muhammad Adam

Ko Kudin Asusun Gwamnatin Kano Kwankwaso Ya Wawushe Baki Daya, Mu Kanawa Mun Yafe Masa, Inji Aisha Muhammad Adam

Siyasa
Ko Kudin Asusun Gwamnatin Kano Kwankwaso Ya Wawushe Baki Daya, Mu Kanawa Mun Yafe Masa, Inji Aisha Muhammad Adam A madadina da kuma sauran ragowar al'ummar jihar Kano ta dabo na zo na ari bakin kowa na ce albasa domin mika sako izuwa ga Maigirma Kwankwaso Madugu Uban Tafiya, Dan Musa Gagara Badau, cewa mu mutanen jihar Kano mun yafe maka koda a ce ka ci wannan kudin da ake fada ka ci, to mu mun yafe. Ka ci bagas, ka ci halak malak. Ai dama dukiyar ta mu ce mu kuma naka ne, to kaida kaya duk mallakar wuya ne. Yau a ce koda asusun gwamnatin Kano ka wawushe ka bar shi babu ko kwandala to mun yafe kasha kuruminka. Muna tare da kai, babu wanda za mu bari ya tozarta ka. Kanawa me za ku ce?

Abubuwan dake sa rama

Kiwon Lafiya
Abubuwan dake sa rama na da yawa amma ga kadan daga ciki kamar haka: Yawan Tunani. Wata cuta ta musamman, kamar su tarin TB, Cutar Kanjamau, da sauransu. Yin Azumi Motsa jiki. Bacci sosai. A rage cin abubuwan da aka sarrafa sosai irin su kayan gwanwani da sauransu. A rage shan kayan zaki irin su lemun kwalba, da chakulet. Shan ruwa da yawa. Cin kayan marmari irin lemu da ayaba, da sauransu. Cin kwai Rage cin abinci da yawa.
Karanta jadawalin makarantun sakandare guda 114 da suka fi dadewa a Najeriya ko makarantarku na ciki?

Karanta jadawalin makarantun sakandare guda 114 da suka fi dadewa a Najeriya ko makarantarku na ciki?

Tarihi
Wadannan jadawalin makarantun sakandare guda 114 ne wanda suka fi dadewa a Najeriya, ko makarantarku na ciki? 1. CMS Grammar School, Bariga, Lagos (1859)2. Methodist Boys High School, Victoria Island, Lagos (1878)3. Methodist Girls High School, Yaba, Lagos (1879)4. Baptist Academy, Obanikoro, Lagos (1885)5. Hope Waddell Training Institute, Calabar (1895)6. St. Anne’s School, (Old Kudeti Girls’ School) Ibadan (1896)7. Oron Boy’s High School, (Old Oron Training Institute) Oron (1897)8. Wesley College of Science (old Wesley College), Elekuro, Ibadan (1905)9. St. Paul’s College, Iyenu, Awka (1900)10. Methodist Boy’s High School, Oron (1905)11. Abeokuta Grammar School, Idi-Aba, Abeokuta (1908)12. King’s College, Catholic Mission Street, Lagos (1909)13. St. John’s School, Bida (1909)14. Alhud...
Kalli Bidiyo: ‘Yan Kwallon Super Eagles sun ki rera sabon taken Najeriya inda suka rera tsohon a wasan da suka buga da Benin Republic

Kalli Bidiyo: ‘Yan Kwallon Super Eagles sun ki rera sabon taken Najeriya inda suka rera tsohon a wasan da suka buga da Benin Republic

Kwallon Kafa
Saidai sun rera tsohon taken wanda aka saba dashi. Kalli Hoton Maryam Yahya da ya jawo cece-kuce, Wani yace mata “dan Allah ki dinga nunawa ke musulmace ko da da daura dankwali ne” https://www.youtube.com/watch?v=rXEIsCimfFM A baya dai 'yan Kwallon sun kasa rera sabon taken a wasan da suka buga da kasar Afrika ta kudu wanda a lokacin da aka sakashi aka gansu sun yi gum.

Meke kawo ruwan nono ga budurwa

Nono
Yawancin abinda ke kawo ruwan nono shine haihuwa. Bayan mace ta haihu, ruwan nononta na zuwa sosai. Bayan haihuwa akwai wasu abubuwan na daban da kan iya kawowa budurwa ruwan nono: Yawan tabawa da matsa nonon budurwa yana iya sawa ya kawo ruwa. Shan wani magani da jikin budurwar be yi amanna dashi ba yana iya sata reaction ruwan nononta ya kawo. A wasu lokutan ma haka kawai babu dalili, nonon budurwa zai iya kawo ruwa. Yanda ake tsayar da zubar ruwan nono Zubar nono na raguwa da kanta daga lokaci zuwa lokaci. Amma akwai abubuwan da za'a iyayi dan magance matsalar. A daina matsa nonon. Wasu lokutan ana gwada daure nonon da tsumma me kyau.