Sunday, December 21
Shadow
Kasar Rasha na takurawa ‘yan Afrika dake kasarta, ko dai su shiga aikin soja, su je yaki da Ukraine ko kuma ta dawo dasu gida

Kasar Rasha na takurawa ‘yan Afrika dake kasarta, ko dai su shiga aikin soja, su je yaki da Ukraine ko kuma ta dawo dasu gida

Siyasa
Rahotanni daga kasar Rasha na cewa, kasar na takurawa 'yan Afrika dake kasar shiga aikin soji dan yin yaki da kasar Ukraine. Rahoton jaridar Bloomberg ya bayyana cewa, kasar ta Rasha tana kuma takurawa hadda dalibai dake karatu a kasar. Saidai duk da haka wasu na baiwa jami'an tsaro cin hanci dan su kyalesu su zauna a kasar ba tare da su shiga aikin sojan ba ko kuma an dawo dasu gida ba. Yakin Rasha da Ukraine dai kullun sai kara kazancewa yake inda Ukraine din ke ci gaba da samun goyon bayan kasashen Yamma da Amurka.
Kalli yanda wannan matar ta suma bata san inda kanta yake ba bayan da aka mata aikin karin girman Duwawu amma yazo da matsala

Kalli yanda wannan matar ta suma bata san inda kanta yake ba bayan da aka mata aikin karin girman Duwawu amma yazo da matsala

Abin Mamaki
Wata shahararriya me amfani da kafafen sada zumunta wadda aka fi sano da Aunty Ramota ta samu matsala bayan zuwa aka mata karin girman duwawu. Yanzu dai tana can ta suma, bata san inda kanta yake ba. Wata ce dai ta dauki nauyin yi mata aiki amma tunda ta ga abin bai yi yanda ake so ba, ta tsere. Wata majiya daga dangin matar ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace tana cikin wani hali.
Subhanallahi: Ji yanda Mahajjaciya ‘yar Najeriya ta kash-she kanta a kasar Saudiyya ta hanyar  fadowa daga sama

Subhanallahi: Ji yanda Mahajjaciya ‘yar Najeriya ta kash-she kanta a kasar Saudiyya ta hanyar fadowa daga sama

Hajjin Bana
Wata Mahajjaciya 'yar Najeriya a kasar Saudiyya ta kashe kansa. An bayyana sunanta da Hajia Hawawu Mohammed kuma ta fito ne daga jihar Kwara. Shugaban hukumar alhazai na jihar, Abdulsalam Abdulkadirne ya bayyana haka inda yace ta fado ne daga gidan bene inda take zaune. Ya kuma ce akwai kuma wani Saliu Mohammed da shima ya rasu a Asibiti. Yace sun yi takaicin faruwar lamarin amma sun sa a ransu cewa kaddara ce daga Allah.
Kalli Hoto: Wannan matar ta Kash-She mijinta bayan da suka yi damfarar Miliyan 250 amma yaki bata kasonta

Kalli Hoto: Wannan matar ta Kash-She mijinta bayan da suka yi damfarar Miliyan 250 amma yaki bata kasonta

Auratayya
'Yansanda a jihar Imo sun kama wannan matar me suna Oluchi Nzemechi,  'yar Kimanin shekaru 27 dake zaune a Uzoagba karamar hukumar Ikeduru ta jihar bayan data kashe mijinta. Matar ta amsa laifinta ba tare da matsala ba. Tace mijinta dan amfarar yana gizo ne kuma itama ya koya mata. Tace sun damfari wani dan kasar Indonesia kudin kasar har Naira Miliyan 250 amma ta yi ta fama da mijinta ya bata kasonta amma yaki shine ta yi amfani da wukar dakin girki ta kasheshi. Tace da farko ta yi rubutu na cewa wanine ya kasheshi har ma yana son yanzu kuma ya koma kan iyalansa ta dora takardar akan gawarsa ta tsere amma duk da haka sai da asirinta ya tonu. Mijin nata dai sunansa Kelechi Nzemechi dan kimanin shekaru 31. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Henry Okoye ya tabbatar da faruwar la...
Bai kamata Tinubu ya soki Gwamnatin Buhari ba saboda cewa yayi zai dora daga inda Buhari ya tsaya>>Buba Galadima

Bai kamata Tinubu ya soki Gwamnatin Buhari ba saboda cewa yayi zai dora daga inda Buhari ya tsaya>>Buba Galadima

Siyasa
Jigo a jam'iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, bai kamata shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dorawa Buhari ko wane irin laifi ba. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a jaridar Sunnewsonline. Yace dalilin da yasa yace haka shine Tinubu yayi Alkawrin dorawa akan inda shugaba Buhari ya gama mulkinsa. Da aka tambayeshi ko me zai ce kan matsin rayuwar da ake ciki, Buba Galadima ya kada baki yace ai 'yan Najeriya ne suka siyowa kansu da kudinsu. Yace sai da ya gargadi mutane amma suka kiya.
Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano

Abuja, Tsaro
'Yansanda a Abuja sun bankado wata maboyar 'yan Bindiga dake gidan Dogo a cikin daji Kweti dake kusa da babban birnin tarayya, Abuja. Kakakin 'yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan ga manema labarai inda tace an bankado maboyar ne bayan samun bayanan sirri. An kama mutane 4 da ake zargi bayan da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron. Dukansu sun amsa cewa su masu garkuwa da mutanene. An kubutar da wasu da suka yi garkuwa dasu inda aka mika su hannun 'yan uwansu.
Bidiyo: Kalli Yanda wasan Rangers da Enyimba ya kare cikin hayaniya, Magoya baya suka cika filin wasan

Bidiyo: Kalli Yanda wasan Rangers da Enyimba ya kare cikin hayaniya, Magoya baya suka cika filin wasan

Kwallon Kafa
Wasan Rangers da Enyimba ya kare cikin tashin hankali bayan da alkalin wasan ya baiwa Rangers bugun daga kai sai me tsaron raga ana kusa da tashi wasan. 'Yan Enyimba dai sun fice daga filin inda hakan ya jawo magoya baya suka cika filin ya hargitse. Kalli Bidiyon a kasa. https://www.youtube.com/watch?v=S2ME11vlABs?si=54C9RceD2gC5A0WD
Ji yanda ake ciki kan maganar mafi karancin Albashi tsakanin Gwamnati da NLC, inda ake tunanin za’a sake komawa yajin aiki

Ji yanda ake ciki kan maganar mafi karancin Albashi tsakanin Gwamnati da NLC, inda ake tunanin za’a sake komawa yajin aiki

Siyasa
Tattaunawa na ci gaba da gudana tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta NLC da TUC inda ake tsammanin za'a karkare a yau. Kungiyar tace ta gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da bukatarta ta a biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin albashi kuma tana jiran ta ji amsa daga gareshi. Saidai matsayar gwamnati shine biyan Naira 62,000 a matsayin mafi karancin Albashin. Shuwagabanni kwadagon sun je Geneva, Kasar Switzerland inda suke halartar taro kan kungiyoyin kwadago na Duniya. Kuma ana tsammanin bayan aun kammala taron, zasu dawo a samu matsaya kan mafi karancin Albashin.
Kalli yanda ‘yan Najeriya suka koma amfani da Cucumber/Gurji wajan yin miya maimakon Tumar saboda tsadar Tumatir din

Kalli yanda ‘yan Najeriya suka koma amfani da Cucumber/Gurji wajan yin miya maimakon Tumar saboda tsadar Tumatir din

Duk Labarai
'Yan Najeriya da yawa sun koma amfani da Gurji, ko kuma Cucumber maimakon Tumatur wajan yin miya. Tumatur dai yayi tsadar da ba'a yi tsammani ba inda ya gagari talaka. An ga yanda aka rika yin miya da Gurji maimakon Tumaturin. https://twitter.com/chude__/status/1799835716891127967?t=oFUgU136aLx5ZXXbp4rUzw&s=19 Me zaku ce?