Sunday, December 21
Shadow

Kwana nawa mace take daukar ciki

Auratayya
Yawanci sai an kai sati 2 zuwa 3 kamin ciki ya shiga bayan jima'i. Ana daukar kwanaki 6 kamin maniyyin namiji da kwan mace su hadu. Bayan haduwarsu ne ciki yake fara kankama. Alamun da ake gane ciki ya shiga shine, daukewar Al'ada. Nonuwa zasu girma ko su kara karfi. Zazzabin safe. Yawan Fitsari. Gajiya. Idan kika ji wadannan alamu zaki iya zuwa gwaji.
An bayyana ranar da mahajjatan Najeriya zasu fara dawowa gida

An bayyana ranar da mahajjatan Najeriya zasu fara dawowa gida

Hajjin Bana
Hukumar Alhazai ta kasa ta bayyana ranar 22 ga watan Yuni a matsayin ranar da Mahajjatan bana zasu fara dawowa gida Najeriya. Shugaban hukumar, Jalal Arabi ne ya bayyana haka ranar Lahadi inda yace jirage 120 ne suka dauki mahajjatan zuwa kasa me tsarki. Yace kuma ranar 222 ga watan Yuni jiragen zasu fara dawo da mahajjatan gida Najeriya. Ya kara da cewa, ba'a yi tsammanin aikin Hajjin bana zai yiyuba amma cikin ikon Allah sai gashi ya faru.

Ministan yaƙin Isra’ila ya sauka daga muƙaminsa

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Ministan yaƙi na Isra'ila, Benny Gantz ya fice daga cikin gwamnatin Netanyahu. Yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai, Mista Gantz ya ce firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya ƙi bari a samu abin da ya kira 'tabbatacciyar nasara' kan Hamas. Ministan ya ƙara da cewa dole ne Mista Netanyahu ya sanya ranar da za a gudanar da zaɓukan ƙasar. Tun a ranar Asabar mista Gantz ya yi niyyar gabatar da jawabin nasa, to amma sai ya jinkirta saboda kuɓutar da wasu Isra'ilawa da sojojin ƙasar suka yi a Gaza. Ficewar jam'iyyarsa daga gwamnatin, ba zai kawo ƙarshen gwamnatin ba, to amma zai ƙara matsin lamba kan mista Netanyahu kan sukar da yake sha a ciki da wajen Isra'ila. Dama dai tun cikin watan Mayun da ya gabata, Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus daga majalisar yaƙin ...

Sudais ya buƙaci maniyyata su zama masu biyayya a lokacin aikin hajji

Hajjin Bana
Babban limamin masallatan Harami Abdulrahman bin Abdulaziz Al-Sudais, ya buƙa ci maniyyata su zama masu bin doka da oda a lokacin gabatar da ayyukan ibadar hajji. Shafin X na Haramain ya ambato Sheikh Sudai na kira ga maniyyatan su zama masu biyayya ga umarnin jami'an tsaro domin tabbatar da gudanar da aikin hajin cikin kwanciyar hankali da lumana. Hukumomin Saudiyya sun ce ya zuwa ranar Lahadi kimanin maniyyata miliyan ɗaya da dubu ɗari uku ne suka isa ƙasar, don gudanar da aikin hajjin na bana.

Sarkin Saudiyya gayyaci Falasɗinawa 2000 zuwa aikin Hajji

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Shugaban masallatan Harami, kuma sarkin Saudiyya, Salman bin Abdul Aziz Al Saud ya bayar da umarnin gayyatar ƙarin 'yan uwan Falasɗinawa 1,000 da aka kashe a Gaza a matsayin baƙinsa. Cikin wata sanarwa da shafin X na Haramain ya wallafa, sarkin ya bayar umarnin ƙarin gayyatar 'yan uwan Falasɗinawa ne domin halartar aikin hajjin bana. Dama dai tun da farko sarkin ya gayyaci wasu Falasɗinawan 1,000, inda a yanzu adadin Falasɗinawan da da aka kashe 'yan uwansu da sarkin ya gayyata ya kai 2,000.
Suma Sanatoci Mafi karancin Albashi ya kamata a biyasu>>Inji Father Mbaka

Suma Sanatoci Mafi karancin Albashi ya kamata a biyasu>>Inji Father Mbaka

Siyasa
Babban malamin Kirista, Father Ejike Mbaka ya bayyana cewa, kamata yayi suma 'yan majalisar tarayya a rika biyansu mafi karancin Albashi. Ya bayyana cewa ma'aikata dakw ainahin wahala wajan aiki amma sune ake biya kudade 'yan kadan inda yace sam hakan bai dace ba. Yace a mayar da mafi karancin Albashin a rika biyan kowa dashi har 'yan majalisar kada a mayar da wasu bayi. Yace saboda menene za'a rika biyan 'yan majalisar Alawus wanda ya wuce ka'ida?
Mu fa har yanzu muna nan kan matsayin mu sai Gwamnati ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi>>NLC

Mu fa har yanzu muna nan kan matsayin mu sai Gwamnati ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi>>NLC

Siyasa
Kungiyar kwadago ta NLC ta jaddada matsayinta na cewa sai Gwamnatin tarayya ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi. Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a inda yace suna jiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauki mataki kan lamarin. Gwamnatin tarayya dai tace Naira 62,000 ne zata iya biya a matsayin mafi karancin Albashin. Saidai Gwamnoni sunce au bazama su iya biyan hakan ba idan dai ba duka kudaden da suke samu bane zasu rika biyan Albashi dashi ba. Yanzu dai abin jira a gani shine yanda zata kaya.