Friday, December 5
Shadow
WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu

WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu

Kano
WATA SABUWA: Lauyoyin Mai Baiwa Shugaba Tinubu Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗo Sun Fitar Da Takardar Maka Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo A Gaban Kotu. Shi dai Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya zargi Nuhu Ribadu ne da baiwa tsigaggen sarkin Kano Aminu Ado Bayero jirgi biyu tare da jami’ań tsáro dan su banƙara a shígar da da shi masarautar Káno. Ya ce kuma Ganduje ne ya je wajań mai bawa shugaban kásar shawara kan harkar tsáro wato Nuhu Ribadu dómin aikata wannań mummunan aiki. A céwar mataimakin Gwamnan duk abinda za muyi zamuyi dan mu tabbatar haka bata faru ba, muna gidan Sarki dukkanin mu jami’an Gwamnati.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa mutanen Kano, Muhammad Sanusi II suke so a matsayin sarki

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta nuna cewa mutanen Kano, Muhammad Sanusi II suke so a matsayin sarki

Kano
Wata kuri’ar jin ra’yin jama’a da aka gudanar a shafin sada zumunta na Twitter ta nuna cewa mafiya yawan mutane Muhammad Sanusi II suke so a matsayin sarkin Kano. Mutane sama da Dubu uku(3000) ne suka bayyana ra’ayinsu akan wannan kuri’ar. Dambarwar sarautar Kano ta ballene bayan da majalisar jihar ta tsige Aminu Ado Bayero ta kuma nada Muhammad Sanusi II a matsayin sabon sarki. Aminu Ado Bayero yaki yadda da saukewar da aka masa inda ya koma Kano, ya kafa fada a gidan Nasarawa. An samu wata kotu data hana tsige Aminu Ado Bayero wadda da wannan ne ya fake yake neman sake komawa kan kujerar sa. Jami’an tsaron Kano sun nuna cewa suna goyon bayan Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kanone inda suka ce umarnin kotu zasu bi.
An bada shawarar cewa, Tunda dai abu yaki ci yaki cinyewa tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero to kawai a hada Musabaka, wanda yaci sai a bashi sarautar

An bada shawarar cewa, Tunda dai abu yaki ci yaki cinyewa tsakanin Sarki Muhammad Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero to kawai a hada Musabaka, wanda yaci sai a bashi sarautar

Kano
A yayin da rikici yaki karewa tsakanin Masu martaba, Muhammad Sanusi II da Aminu Ado Bayero, an kawo wata shawara da zata iya zama mafita ga lamarin. An bada shawarar cewa a hada sarakunan biyu wanda kowanne ya doge akan bakarsa shine sarkin Kano a basu musabakar karatun Qur’ani. Duk wanda yaci sai a bashi sarautar Kano. Shafin Kwankwasiyya ne ya kawo wannan shawara. Sarki Muhammad Sanusi II dai shahararren malamin addini ne wanda yana tafsiri kuma shine ke hudubar juma’a. Idan dai za’ yi wannan musabaka, ga dukkan alamu shine zai yi nasara.
WATA SABUWA: An Bankaɗo Cewa Babu Sa Hannun Alƙalin Da Ake Iƙrarin Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sanusi II

WATA SABUWA: An Bankaɗo Cewa Babu Sa Hannun Alƙalin Da Ake Iƙrarin Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sanusi II

Kano
WATA SABUWA: An Bankaɗo Cewa Babu Sa Hannun Alƙalin Da Ake Iƙrarin Ya Dakatar Da Naɗin Sarki Sanusi II. Domin a lokacin ma an ce Mai Shari’a A.M Liman yana Amurka Kamar yadda fitaccen ɗan jaridar nan Ja’afar Ja’afar ya bayyana a shafin sa ya nuna bambancin dake jikin sa hannun da Jostice A. M. Liman yake yi a duk lokacin da ya yi hukunci da kuma wanda ake yaɗawa yanzu. Ya ce: Kwatanta sa hannun mai shari’a Liman na yau da kullum, da kuma na dokar da ake amfani da shi yanzu wajen kawo rashin zaman lafiya a Kano ku ga bambancin. Shin alkali ya canza sa hannun sa ko ya ba wani izini ya canza shi? ~ Cewar Jaafar Jaafar
Kai Talaka Da Kake Ta Tada Jijiyar Wuya Kan Ŕìķìçìn Masarautar Kano, Ina Kake A Cikin Wannan Hoton?

Kai Talaka Da Kake Ta Tada Jijiyar Wuya Kan Ŕìķìçìn Masarautar Kano, Ina Kake A Cikin Wannan Hoton?

Kano
Kai Talaka Da Kake Ta Tada Jijiyar Wuya Kan Ŕìķìçìn Masarautar Kano, Ina Kake A Cikin Wannan Hoton? A cikin hoton; Akwai Dan Sarki Sunusi.Akwai Dan Sarki Aminu.Akwai Dan Sarki Nasiru.Akwai Dan gidan Ciroma.Akwai Dan gidan Falaki. Kai talaka da kake tada jijiyar wuya da zagi da cin mutuncin juna akan masarautar Kano, don Allah ina kake a cikin wannan hoton? Daga Comr Abba Sani Pantami
‘Yansanda na bi gida-gida dan kama ‘yan daba dake shirin kai hari majalisar jihar Kano

‘Yansanda na bi gida-gida dan kama ‘yan daba dake shirin kai hari majalisar jihar Kano

Duk Labarai, Kano
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, ‘yansanda na bi gida-gida suna kama matasa da ake zargin na shirin kai hari majalisar jihar Kano. Hakan na da nasaba da Sauke Aminu Ado Bayero da majalisar ta yi daga kan kujerar Sarautar Kano. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana hakan. Ya bayyana hakane da yammacin ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai. Ya bayyana wadanda ke shirin kai harin da cewa, makiyan jihar Kanone.