Thursday, July 2
Shadow

Amfanin karkashi a gashi: Yadda ake wanke kai da karkashi

Gyaran Gashi
Ga yanda ake amfani da Karkashi dan gyaran gashi. Akwai hanyoyi da yawa, ga kadan daga cikinsu: Da farko zaki samu busasshen karkashi ki dakeshi aturmin qarfe sai kisa ruwa mai zafi a bap Na wanka sai ki zuba karkashin Dan dadai sai ki zuba shampoo sai ki saka ruwan toka ko kanwa sai ki kada zakiga yayi kumpa sosai kuma yayi kore shar sai ki tsaga tsakiyan Kai ki raba gashi biyu sai kisa ta sunkuyo cikin bap din sai ki qulle gefe daya ki wanke dayan ruwa ya shiga sosai ki Mirza da kyau sai ki matseshi ki dauko cokali idan kika matse sai ki katse shi da cokali ruwan yana bin jikin cokali har sai kinga ya daina sai ki daure shi sai kiyima dayan gefen ma haka. Idan ya bushe kika taje kan zakiga idan da akwai abin karkashin zai fita sai ki samu mai oil ko zai tun ki shafa shknn Note...

Gyaran gashi da ruwan shinkafa

Gyaran Gashi
Mutanen kasar China da Japan sun dade suna amfani da ruwan shinkafa wajan kara tsawon gashi da kuma hanashi yin furfura. Hakanan kuma a wani kaulin,ruwan Shinkafa na hana gashin mumurdewa da hadewa da juna. Hakanan kuma ruwan shinkafa na karawa gashin kai sheki. Matan wani kauye a China me suna, Huangluo na daga matan da suka fi kowane mata tsawon gashi a Duniya inda aka ruwaito cewa gashin kansu hana kai tsawon kafa 6. Sannan kuma gashin kansu yawanci bai fara yin furfura sai sun kai kusa da shekaru 80 a Duniya. Wadannan mata sun bayyana cewa sirrinsu shine wanke gashin kansu da suke yi da ruwan shinkafa. YANDA ZA'A SAMU RUWAN SHINKAFA DAN GYARAN GASHI Akwai hanyoyi 3 da ake samun ruwan shinkafa dan gyara gashi dashi. Danyar Shinkafa: Ana samun danyar Shinkafa rab...
Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri

Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana’antar Kannywood, A’isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri

Kannywood
INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRAJI'UN Allah Ya yi wa Hajiya Hauwa, yayar mahaifiyar jarumar masana'antar Kannywood, A'isha Humaira, ràsųwa a birnin Maiduguri. Humaira ta bayyana rasuwar a shafinta na Instagram inda ta nemi al'ummar musulmi da su sanya ta cikin addu'a Allah Ya gafarta mata tare da sauran al'ummar Annabi (S.A.W) da suka riga mu gidan gaskiya. Za a yi mata sallar Jana'iza a gobe da safe, a birnin Maiduguri na Jihar Borno.

Hadin tsawon gashi

Gyaran Gashi
Hadin tsawon gashi Akwai hanyoyi da dama da mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo. Abu ne mai sauki. Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya. Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau don haka, ya kamata mu kula da gashinmu sosai. Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko , wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi. Ina son a san cewa wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, ba ya kamata ana hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai a ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Abubuwan da za a bukata Man AmlaZumaRuwan dumiHadi A zuba cokalin amla biyu a roba.Sannan sai a zuba rabin cokalin ...

Tsawon gashi cikin sati daya

Gyaran Gashi
Ana iya samun tsawon gashi cikin sati daya idan aka yi abinda ya dace kamar yanda zamu yi bayani a kasa: Hanya ta farko da ake iya kara gashi cikin sati daya itace ta amfani da man kwakwa, ko man Zaitun. Yanda ake yi shine, ana samun man kwakwa ko kan zaitun a dafashi, a sauke ya huce,amma kada a bari ya huce gaba daya, sai a taba da hannu a ji idan akwai dumi yayi daidai yanza za'a iya shafawa akai sai a rika dangwala ana shafawa akai, a shafa sosai ya shiga cikin gashi da kyau. A tabbatar an gauraye duka gashin dashi. A bari yayi mintuna akalla 30 sannan a wanke da shampoo. Hakanan masana sun kara da cewa, cin abinci me gina jiki da kyau da kuma motsa jiki da kuma murza gashin kai akai-akai watau a rika yi mai tausa har zuwa inda ya tsiro yana taimakawa kara yawan gashi sos...

Gashin gaba

Tsafta
Gashin Gaba ko kuma ace gashin mara gashine dake fitowa a jikin farjin mace da kuma azzakarin namiji wanda alamace dake nuna cewa mutum ya fara girma kuma ya balaga kuma hukuncin shari'a ya hau kansa. Tsaftace gashin gaba yana da muhimmanci dan yana sakawa mutum ya rika samun nutsuwa sannan kuma yana taimakawa wajan hana warin gaba. Yana da kyau a aske gashin gaba, ko da ba'a aske duka ga, a rika rage masa tsawo daga lokaci zuwa lokaci. Sannan kuma idan an barshi a rika wankeshi akai-akai dan idan ba'a kula dashi za'a ga ya kan rika daukar datti ya canja kala ya koma ruwan kasa, har ya rika wari.

Ya halatta shan maniyyi

Magunguna
Ra'ayin Malumma sun banbanta kan shan maniyyi. Wasu malaman suna ganin tunda abu ne wanda baizo cewa magabata sun aikata ba, ya kamata a kyamaceshi. A takaice ma, wasu na ganin cewa al'aurar namiji na da najasa wadda bai kamata a rika sakata a baki ba dan zata iya cutarwa dan haka suka ga barin yin hakan yafi yinsa Alkhairi. Akwai kuma malaman dake ganin idan mutum zai iya yana iyayi ba laifi. A bangare guda kuma, Tabbas Maniyyi na da sinadarai masu karawa jiki amfani, saidai masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, sinadaran basu da yawan da zasu yiwa jikin Tasiri. To zabi dai ya rage ga mutum ko dai yayi ko kar yayi.

Amfanin toka a hammata

Magunguna, Tsafta
Toka na da amfani sosai wajan gyara hammata da hanata wari. Ana amfani da Toka da Lemun tsami wajan tsaftace hammata dan hanata wari da zufa kuma wannan dabarace da aka yi amfani da ita shekaru aru-aru da suka gabata. Ga yanda ake yi kamar haka: Ana samun lemun tsami. Sannan a samu Toka ta itace ko gawayi. A tace tokar sannan a matse lemun tsamin a cikinta, a kwaba, sannan a shafa a hamatar. A bari yayi kamar minti biyar sannan a wanke. Ana iya yin hakan sau 2 a sati. Saidai idan bai karbi fatar ki ba a dakata amfani dashi, misali idan yana sanya yawan kaikai a hamatar ko yana kawo kuraje. Sai a daina a yi amfami da sauran dabarun tsaftace hamata na kasa: YADDA ZA A TSAFTACE HAMMATA Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin namu na kwalliya. A yau n...