Saturday, December 20
Shadow
Mu fa har yanzu muna nan kan matsayin mu sai Gwamnati ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi>>NLC

Mu fa har yanzu muna nan kan matsayin mu sai Gwamnati ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi>>NLC

Siyasa
Kungiyar kwadago ta NLC ta jaddada matsayinta na cewa sai Gwamnatin tarayya ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi. Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a inda yace suna jiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauki mataki kan lamarin. Gwamnatin tarayya dai tace Naira 62,000 ne zata iya biya a matsayin mafi karancin Albashin. Saidai Gwamnoni sunce au bazama su iya biyan hakan ba idan dai ba duka kudaden da suke samu bane zasu rika biyan Albashi dashi ba. Yanzu dai abin jira a gani shine yanda zata kaya.
A karshe dai Sarkin Waka ya bayar da hakuri, Saidai ya fito da sabuwar karin magana

A karshe dai Sarkin Waka ya bayar da hakuri, Saidai ya fito da sabuwar karin magana

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Nazir Ahmad Sarkin Waka ya fito da sabuwar karin magana wadda ya jefawa 'yan Cryptocurrency. Nazir a shafinsa na sada zumuntar Instagram yace "Ta nan muka fara wai maroki ya ga dan Mining." Ya kara da cewa, "yace ai duk zuciyar daya ce ma'ana a mace" A karshe dai yace ba zai sake yin magana ba amma idan ya baiwa wani haushi a yi hakuri
Ba zata fashe ba>>Nazir Sarkin Waka ya kara tsokanar ‘Yan Crypto

Ba zata fashe ba>>Nazir Sarkin Waka ya kara tsokanar ‘Yan Crypto

Kannywood, Nazir Ahmad Sarkin Waka
Tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka ya bayyana cewa, Cryptocurrency ba zata fashe ba. Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta a yayin da ake ci gaba da yakin cacar baki ta yanar gizo shi da 'yan Crypto. Nazir ya kuma kara da cewa ita tunatarwa tana amfanine amma fa ga mumini kuma shi Munimi ba'a cizonsa sau biyu a rami daya. Yace idan Pi bata fashe ba ta yaya wannan zata fashe?
Ba Zan Iya Bada Auran Ƴata Ga Wanda Bashi Da Kuɗi Ba (Talaka) – Kabiru, Dallah

Ba Zan Iya Bada Auran Ƴata Ga Wanda Bashi Da Kuɗi Ba (Talaka) – Kabiru, Dallah

Auratayya
Kowane mutum yana neman ajinsa na budurwa haka matar dazai aura, don haka ina kira ga maza dasu daina kiran mata mayun kuɗi, rayuwa mai daɗi babu wanda bayaso ya tsinta kanshi ciki, da hakane na yanke shawarar ni dai ba zan iya bada ƴata ga wanda bashi da kuɗi ba ko tarin abin duniya. Wannan ra'ayine na kaina kuma idan ba ku ji daɗin hakan ba to kuna da damar rungumar taransfoma mafi kusa daku - Kabiru Ibrahim Dallah, dan kasuwan Najeriya matashin ɗan kasuwa a Nijeriya. Ko mene zaku ce?
Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sandan Isra’ila

Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sandan Isra’ila

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Siyasa, Yakin gaza da isra'ila
Masu zanga-zangar ƙin jinin gwamnati sun yi taho mu gama da ƴan sanda, a daidai lokacin da ake gangamin a sassan Isra'ila kan kiran a kuɓutar da sauran waɗanda ke hannun Hamas. Sai dai mai magana da yawun sojin ƙasar,Rear admiral Daniel Hagari ya ce su na ƙoƙari kan batun. Ya ce dakarun Isra'ila sun ɗauki makwanni su na shirye-shiryen aikin nan, an ba su horo kan yadda za su kuɓutar da mutanenmu, ba za mu gaji ba har sai sauran sun dawo. Masu zanga-zangar su na sukar firaiminista Benjamin Netanyahu, wanda ke ganawa da iyalan waɗanda aka saka maimakon waɗanda ke cikin tashin hankali da rashin tabbacin ko nasu ƴan uwan za su dawo gida a raye.
NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi da aka shigar da su Najeriya daga India

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi da aka shigar da su Najeriya daga India

Siyasa
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA ta ce jami'an ta sun kama kwalba 175,000 ta miyagun ƙwayoyi da maganin tari da aka shigar da su ƙasar daga India. Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce sun yi wannan nasarar ne mako guda bayan wata irin ta da suka samu, inda suka kama hodar ibilis da aka shiga da ita Najeriyar, a jihar Rivers. Ya yi bayanin cewa NDLEA da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro ta yi nasarar kama kayan laifin ne a ranar juma'a, 7 ga watan Yunin bana, bayan sun nemi gudanar da cikakken bincike a kan kayan da aka shigo dasu daga ƙasashen waje. Babafemi ya kuma bayyana cewa akwai sauran kayan laifi da suka haɗa ga kƙwaya da tabar wiwi da hodar ibilis da jami'an NDLEA suka kama a sassan Najeriya, a cikin makon da ya gabata. Ya ce daga cikin ...
Babbar Sallah: Gwamnatin jihar Sokoto ta amince a biya albashin watan Yuni

Babbar Sallah: Gwamnatin jihar Sokoto ta amince a biya albashin watan Yuni

Siyasa, Sokoto
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince a biya albashin watan Yuni ga ma'aikatan jihar daga ranar Litinin. Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin bai wa ma'aikatan gwamnatin jihar damar yin bikin babbar sallah cikin walwala. Sakataren yaɗa labaran gwamnan Sokoto, Abubakar Bawa, ya ce dukkan ma'aikatan jihar, da na ƙananan hukumomi da kuma ƴan fansho ne za su amfana da wannan karamci. Abubakar Bawa, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da biyan albashin ma'aikata a kan lokaci, kamar yadda ya ce ya zama al'adar gwamantin, biyan albashi a ranar 20 zuwa 21 na kowanne wata, tun bayan karɓar ragamar mulki. Dama dai gwamnonin jihohin Arewa sun saba yin irin wannan karamci idan aka samu yanayi na gudanar da shagulgulan sallah amma wata bai ƙare ba.
‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

‘Yan sanda sun kama mutum huɗu kan zargin garkuwa da mutane a dazukan Abuja

Tsaro
Rundunar 'yan sandan birnin Abuja, tare da haɗin gwiwa dakarun sahen yaƙi da manyan laifuka da 'yan sanda farin kaya, da mafarauta, sun wargaza sansanonin wasu 'yan bindiga a ƙauyen Gidan Dogo da dajin Kweti da ke kan iyakar Abuja da Kaduna. Cikin wata sanarwar jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sandan birnin, SP Josephine Adeh, ta fitar ta ce bayan samun bayanan sirri, jami'an tsaron suka kai samame dajin ranar 7 ga watan Mayu, in da suka kama mutum huɗu da suke zargi. Sanarwar ta ce mutanen da suka kama, sun faɗa wa 'yan sanda cewa suna cikin wani gungun masu garkuwa da mutane mai suna, 'Mai One Million', waɗanda suke da alhakin kai hare-hare tare da garkuwa da mutane a birnin Abuja da kewaye. 'Samamen wanda aka samu musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, ya tilasta wa 'ya...