Friday, December 19
Shadow
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu

Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu

Siyasa
Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan kuɗi, Wale Edun, da ya fito da abubuwan da za a kashe akan sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwanaki biyu. Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawar da tawagar ta yi da shugaban ƙasar a Aso Rock Villa, a ranar Talata.
WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya’a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya’a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi

Kano
WATA SABUWA: Babu Wanda Muka Yi Wa Mubaya'a Tsakanin Sarki Sanusi II Da Sarki Aminu Ado Bayero, Cewar Iyalan Sheikh Dahiru Bauchi Sayyadi Muktar Ibrahim Dahiru Bauchi ya musanta labarin da wasu jaridu suka wallafa cewar sun je sun yi wa Sarki Sunusi II mubaya'a sannan suka kara yi wa Sarki Aminu Ado Bayero mubaya'a. A cewar sa sun kai ziyarar ne karkashin wata kungiya da Sheikh Aminu Dahiru Bauchi ke jagoranta na hadin kan al'umma musulmi tare da samar da cigaba, inda daga nan suka kuma kaiwa Sarki Aminu ziyara domin jajantawa akan abun da ya faru da shi. "Mu ba mu dauki bangare ba, kawai muna fatan Allah ya kawo dauki ne akan abun da ke faruwa a Kano, domin duk wani Musulmi a Arewa ba zai ji dadin abun da ke faruwa ba a Gidan Dabo", inji SayyadiMukhtar Ibrahim Sheik Dahiru Ba...
Ba zamu amince da kari dan kadan ba akan Dubu 60>>NLC

Ba zamu amince da kari dan kadan ba akan Dubu 60>>NLC

Siyasa
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, ba zata amince da kari dan kadan, wanda bai kai ya kawo ba akan Naira Dubu 60 ba. Kungiyar Kwadago ta NLC dai ta amince ta dakatar da yajin aikin da take dan bayar da dama ga gwamnati ta mata kari akan Naira Dubu 60 na mafi karancin Albashi. Shugaban kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata ganawa da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV. Yace su basu nace wai sai an biyasu Naira Dubu dari hudu ba amma dai abinda suke cewa, shine a biyasu albashi me kyau.
Mun kunno wutar lantarki bayan janye yajin aiki – Ma’aikatan lantarki a Najeriya

Mun kunno wutar lantarki bayan janye yajin aiki – Ma’aikatan lantarki a Najeriya

Duk Labarai
Ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta ƙasa a Najeriya ta ce an sake kunna babban layin wutar da aka kashe bayan janye yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka yi.Shugaban ƙungiyar National Union of Electricity Employees (NUEE), Adebiyi Adeyeye, ya faɗa wa jaridar Punch cewa sun kunna layin ne bayan janye yajin aikin a safiyar yau."An janye yajin aiki kuma hakan yana nufin layin ya koma aiki yadda ya dace. An kunna shi tuni," in ji Mista Adeyeye.Sai dai har yanzu akasarin ƙasar na cikin duhu duk da wannan iƙirari da shugaban ya yi.Tun a jiya Litinin kamfanin kula da rarraba lantarki a Najeriya TCN ya ce mambobin ƙungiyar ƙwadago ne suka tilasta wa ma'aikatan lantarkin shiga yajin aikin ta hanyar kashe babban layin.
Ƙasa ta rufe mutum 30 a mahaƙar ma’adanai ta jihar Neja

Ƙasa ta rufe mutum 30 a mahaƙar ma’adanai ta jihar Neja

Jihar Naija
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja a Najeriya (NSEMA) ta ce kimanin mutum 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta auku a wani wurin hakar ma’adinai. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Galkogo na ƙaramar hukumar Shiroro. Hukumar ta ce an kuma samu nasarar ceto mutum shida da rai, sai dai sun samu munanan raunuka. Mahakar dai ta rufta ne a jiya Litinin lokacin da suke tsaka da aiki haƙar ma'adanai. Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zubairu Ahmad:
Zan samu ribar Dala Biliyan $30 a karshen shekarar 2024>>Dangote

Zan samu ribar Dala Biliyan $30 a karshen shekarar 2024>>Dangote

Kasuwanci
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa nan da karshen shekarar 2024 zai samu ribar zunzurutun kudi har Dala Biliyan $30. Dangote ya bayyana hakane a hirar da CNN ta yi dashi. Ya bayyana cewa, hakan zai sa kamfaninsa ya shiga sanun kamfanoni 120 mafiya karfi a Duniya. Dangote dai a yanzu yana da mamatar man fetur wadda take daya daga cikin matatun man da ke da girma a Duniya.
Hotuna da Bidiyo: Ya baiwa ‘yan mata 2, kawaye miliyan 1 su je yayi lalata dasu, saidai ya kash-she su ya yi tsafi dasu

Hotuna da Bidiyo: Ya baiwa ‘yan mata 2, kawaye miliyan 1 su je yayi lalata dasu, saidai ya kash-she su ya yi tsafi dasu

Tsaro
Wasu 'yan mata da suka dauki hankula a kwanannan su biyu kawayen juna sun je wajan wani mutum dan yin lalata. Saidai tin da suka tafi wajensa ba'a sake ganinsu ba. Hakan yasa aka yi kiyasin cewa sun bata. Saidai daga baya an gano mutumin inda aka kamashi. Amma ana kan hanyar da za'a kaishi ofoshin 'yansanda, sai ya yi kokarin tserewa wannan yasa 'yansandan suka kasheshi. An gano cewa, mutumin yana da alaka da wata kungiyar Asiri. Wasu karin bayanai da suka bayyana kan lamarin sun nuna cewa, mutumin ya baiwa 'yan matan Naira Miliyan daya ne dan su je yayi lalata dasu. Saidai ashe ajali ne yake kiransu. Labarin wadannan 'yan mata biyu dai sai ci gaba da kara daukar hankaki yake, domin kuwa zuwa yanzu an gano gawarwakinsu a kusa a gidan mutumin da ya gayya...