Friday, December 19
Shadow
Kuma dai: Kasar Israela bata daddara ba, ta sake kai harin da ya kashe sojan kasar Iran

Kuma dai: Kasar Israela bata daddara ba, ta sake kai harin da ya kashe sojan kasar Iran

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Tsaro, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Israela ta kai wani mummunan hari a birnin Aleppo na kasar Syria da kashe mutane da yawa ciki hadda wani sojan kasar Iran. Saidai zuwa yanzu, kasar ta Israela bata kai ga bayyana cewa itace ta kai harin ba. Wannan ne dai hari na farko tun bayan na 1 ga watan Afrilu wanda Israelan ta kai kan babban birnin Syria, Damascus wanda yayi sanadiyyar mutuwar sojojin kasar Iran. A wancan lokaci dai, kasar Iran din ta mayar da martani ta hanyar jefawa kasar Israela makamai da yawa wanda sai da kasashen Amurka, ingila da Faransa suka taru suka taresu. Wannan karin kuma ba'a san wane mataki ne kasar Iran din zata dauka akan wanan harin da Israelan ta kai mata ba.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Yace Ya Bada Umarnin Gyaran Dukkanin Hanyoyin Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Yace Ya Bada Umarnin Gyaran Dukkanin Hanyoyin Jihar Kano

Siyasa
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Yace Ya Bada Umarnin Gyaran Dukkanin Hanyoyin Jihar Kano Sakamakon karatowar lokacin damuna a yanzu haka gwamnan jihar Kano ya bayar da umarni ga hukumar dake kula da titunan jihar Kano akan a tabbata duk wani titi daya samu fashewa ko zaizayewa a cikin birnin Kano a tabbatar an gyara shi domin samun nutsuwa ga masu ababen hawa. Wannan umarni da gwamnan ya bayar tuni ya fara aiki domin kuwa tuni hukumar ta KARMA ta fara aikin gyare-gyaren titunan da suka samu matsala.
Majalisar kasar Amurka ta amince da kudirin dokar da zai kakabawa kotun Duniya takunkumi saboda yunkurin ta na son kama shugaban Israela, Benjamin Netanyahu

Majalisar kasar Amurka ta amince da kudirin dokar da zai kakabawa kotun Duniya takunkumi saboda yunkurin ta na son kama shugaban Israela, Benjamin Netanyahu

Siyasa
Majalisar kasar Amurka ta amince da kudirin dokar da zai kakabawa kotun duniya takunkumi saboda hukuncin kama shugaban Israela kan kisan da yakewa Falas-dinawa. Wanda ke son a amince da wannan doka gida 247 ne sai kuma wanda basa so 155 ne wanda akan yasa kudirin ya zama doka. Dokar ta tanadi hana Visa da kuma sauran takunkumi ga duk wanda ke aiki da kotun da kuma wanda ke baiwa kotun kudin gudanarwa.
Madrid za ta tattauna da Nacho, Chelsea na zawarcin Sesko

Madrid za ta tattauna da Nacho, Chelsea na zawarcin Sesko

Wasanni
Kyaftin ɗin Real Madrid da ya lashe gasar zakarun Turai, Nacho, mai shekara 34, zai gana da ƙungiyar domin tattauna makomarsa indan kwantiragin ɗan wasan na sifaniya ya ƙare a wannan bazarar. (The Athletic) Chelsea na da ƙwarin gwiwar cewa za ta iya fafatawa da Arsenal a yunƙurin sayen ɗan wasan gaban Slovenia Benjamin Sesko mai shekara 21 daga RB Leipzig. (Standard) Arsenal na nazari kan ɗan wasan Girona da Ukraine Viktor Tsygankov, mai shekara 26, wanda AC Milan ke zawarci. (Sport) Manchester United na sha'awar sayen dan wasan bayan Everton da Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 21, yayin da ta ke neman ƙarfafa ƴan wasanta na baya. Kuma tana zawarcin ɗan wasan baya na Juventus da Brazil Gleison Bremer, mai shekara 27, da ...
Hoto: An Ķàśhè Wannan Šòjan Tare Da Kwace Masa Waya A Unguwar Sarki Dake Kaduna

Hoto: An Ķàśhè Wannan Šòjan Tare Da Kwace Masa Waya A Unguwar Sarki Dake Kaduna

Tsaro
INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN An Ķàśhè Wannan Šòjan Tare Da Kwace Masa Waya A Unguwar Sarki Dake Kaduna SUN YI Kl$AN KAI AKAN WAYA Wasu barayi a Unguwar Sarki Kaduna sun tare wannan Matashin ofisan Soja Lt. Isah M Abubakar akan hanyarsa na zuwa gida suka ka$he shi bayan sun kwace wayarsa Wani irin rashin imani ne wannan, a ka$he mutum saboda kawai a kwace wayarsa kuma Soja?Gaskiya akwai abin tsoro sosai game da makomarmu anan gaba Allah Ka jikansa, Ka gafarta masa, Ka karemu daga sharrin masu sharri da cutarwa.
Hukumar ‘yansanda ta saki sunayen mutane dubu 10 da suka yi nasara wajen neman aikin

Hukumar ‘yansanda ta saki sunayen mutane dubu 10 da suka yi nasara wajen neman aikin

Tsaro
Hukumar 'yansanda ta PSC ta saki bayanan mutane dubu 10 da suka yi nasarar tsallakewa mataki na gaba a neman aikin dansandan. Mutane 61,092 ne dai aka ajiye gefe wanda basu tsallake ba zuwa wannan matsayi. Hukumar tace dan tabbatar da an yi adalci wajan fitar da sunayen ta yi aiki tare da majalisar tarayya, da hukumar tabbatar da an yi raba daidai wajan bada aikin gwamnati, da kuma hukumar 'yansanda. Tace ta tabbatar an baiwa kowace karamar hukuma a Najeriya cikin 774 da ake dasu damar wakilci a cikin wadanda aka dauka din. Shugaban hukumar, Ikechukwu Ani ne ya bayyana hakan.
Farashin Naira zai tsaya akan 1,450 akan kowace dala

Farashin Naira zai tsaya akan 1,450 akan kowace dala

Siyasa
Wata hukumar dake saka ido akan farashin kudaden Duniya, Fitch Ratings ta yi hasashen cewa, farashin Naira zai kare akan 1,450 ne akan kowace dala har zuwa karshen shekarar 2024. Daraktan hukumar, Gaimin Nonyane ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi dashi kan Najeriya da kasar Misra/Egypt. Ya kara da cewa, har yanzu Naira bata daidaita ba akan farashi daya tun bayan da aka cire tallafin dala. Yace zuwa shekara me zuwa ma Nairar zata ci gaba da faduwa amma ba zasu iya bayyana a farashin da zata tsaya ba.
Gwamnoni sun kashe Naira Biliyan dari tara da sittin da takwas(968,000,000) wajan Shan kayan zaki da Alawus din taruka a watanni 3 da suka gabata

Gwamnoni sun kashe Naira Biliyan dari tara da sittin da takwas(968,000,000) wajan Shan kayan zaki da Alawus din taruka a watanni 3 da suka gabata

Siyasa
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Najeriya 30 sun kashe Naira biliyan dari tara da sittin da takwas, N986.64bn wajan shan kayan ruwa da alawus din taruka da tafiye-tafiye da sauransu. Watau dai wadannan kudade ba'a kashesu kai tsaye wajan yin wani aiki da zai amfani al'uma ba. An samo wadannan bayanai ne daga kundin tattara bayanan yanda gwamnati ke kashe kudaden kasa saidai babu bayanan jihohi 6, Benue, Imo, Niger, Rivers, Sokoto da kuma jihar Yobe. Bayanan sun nuna cewa jihohi 3 din sun kashe Naira Biliyan 5.1 wajan baiwa baki kayan ruwa watau lemu da ruwan sha da sauran kayan zaki. Sannan sun kashe Naira Biliyan 4.67 a matsayin Alawus ga ma'aikatan gwamnati. Jihohin sun kuma kashe Naira Biliyan 34.63 wajan tafiye-tafiye a cikin gida da kasashen waje hakanan kuma sun k...
Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote

Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote

Kasuwanci
Babban Attajirin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana cewa, kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya basa son sayar masa da danyen man fetur din. Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na CNN suka yi dashi inda yace kamfanonin sun saba da kai man fetur kasashen waje suna samun kudi dan haka sun ki sayar masa da danyen man. Yace da za'a sayar masa da danyen man, babu bukatar a rika sayo tataccen man daga kasashen turawa. Yace amma 'yan kasuwa dake shigo da man fetur din daga kasashen waje basa son hakan dan kuwa zasu rasa aiki. Saidai gwamnatin Najeriya ta bakin hukumar dake kula da harkar man fetur din, NUPRC, ta bayyana cewa zasu shiga tsakanin Dangote da kamfanonin dake hako man fetur din. Wakilin hukumar, Olaide Shonola ne ya bayyana haka a hirar da jaridar Punch ta yi...
‘Yan majalisar tarayya dake jam’iyyun Adawa sun nemi Gwamnati data biya ma’aikata Naira Dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

‘Yan majalisar tarayya dake jam’iyyun Adawa sun nemi Gwamnati data biya ma’aikata Naira Dubu dari(100,000) a matsayin mafi karancin Albashi

Siyasa
'Yan majalisar tarayya dake jam'iyyun Adawa irin su PDP, Labour party da sauransu, sun yi kiran cewa, ya kamata gwamnati ta biya ma'aikata Naira dubu 100 a matsayin mafi karancin Albashi. Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a gidan jaridar Punch. Yace a halin da ake yanzu, duk albashin da za'a biya dake kasa da Naira 298,000 ba zai kai ma'aikaci ko ina ba. Ya kara da cewa, kasa biyan albashin da zai ishi ma'ikata yin rayuwa me kyau, sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya ne.