Thursday, March 5
Shadow

Menene sunan awara da turanci

Sunaye
Sunan Awara da turanshi shine Soybean cake. Awara na daya daga cikin abunci masu arha da ake amfani dasu wajan kawar da yunwa cikin gaggawa a arewacin Najeriya. Hakanan ana cin awara dan marmari. Kasancewar ana amfani da waken suya ne wajan yinta, yana taimakawa sosai wajan gina jiki.

Menene sunan alkama da turanci

Sunaye
Sunan Alkama da turanci shine wheat. Ana sarrafa Alkama ta hanyoyi daban-daban a al-adu daban-daban na Duniya. Misali a Arewacin Najeriya, ana sarrafa alkama a yo tuwon furfushe, Burabusko, Fankaso, Fulawa da sauransu. Alkama na daya daga cikin abubuwan daka fi ci a fadin Duniya baki daya.

Kalolin ruwan gaban mace

Gaban mace
Kin taba tunanin ko kalolin ruwan dake fita daga gaban mace guda nawane? A wannan rubutun,mun kawo muku cikakken bayani kan yawan kalolin ruwan dake fita daga gaban mace da kuma ma'anar kowanne. Ga su kamar haka: Ruwan dake fita a gaban mace abune da yawancin mata sun saba dashi, kuma yana fitane dan wanke da tsaftace gaban macen daga lokaci zuwa lokaci. Ba abune na tashin hankali ba amma ya kamata a lura da canje-canje a kalolin ruwan da kuma yanayin jiki wanda ka iya sanyawa a gane shigar cuta. Fitar Farin Ruwa: Farin ruwa wanda wani lokacin yakan iya zama me yauki ko me ruwa-ruwa a gaban mace bashi da matsala. Wani lokacin ma zaki ga ya bata miki wando, a wani lokacin ida kina jin sha'awa zaki iya jin wannan ruwa wanda yana zuwane dan saukaka yin jima'i. Hakanan kum...

Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 8 a Maiduguri da jikkata wasu da dama

Borno, Tsaro
Rahotanni daga jihar Borno na cewa harin Bom ya kashe akalla mutane 8 da jikkata mutane da dama. Harin wanda na kunar bakin wakene mahara 4 ne suka kaishi kuma rahoto yace dukansu sun mutu. Hukumar 'yansandan jihar ta tabbatar da mutane 8 ne suka mutu inda wasu 15 suka jikkata. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya bayyana cewa lamarin ya farune da misalin karfe 3:40 na safiyar yau,Rabar, 29 ga watan Yuni. Rahoton yace wata mata dake goye da yaro ta tayar da bom din a tashar motar Mararraba dake T. Junction dake garin Gwoza. Matar da dan da take goye dashi da wasu 6 sun mutu. A bangaren jaridar Premium times kuwa, tace mata 4 ne suka tayar da bamabamai a bangarori daban-daban na jihar wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba'a kai ga tantance yawansu ba c...

Fitar farin ruwa mai kauri

Gaban mace
Idan a lokacin jinin hailarki ne farin ruwa mai kauri ke fita daga gabanki, to babu matsala. Amma idan ba lokacin haila bane, zai iya zama matsalar rashin lafiya. Fitar ruwa a gaban mace alamace ta lafiyar gaban watau farji. Yawanci duk farin ruwan da zaki ga yana fita daga gabanki a lokacin jinin al'ada ba alama bace dake nuna akwai matsala ba, hakan na nuna al'aurarki ko gabanki bashi da matsala. Amfanin wannan ruwa dake fitowa daga gabanki yana taimakawa fatocin dake cikin gabanki wajan yin laushi sosai a lokacin jinin al'ada da kuma lokacin da kike dauke da ciki. Hakanan wannan ruwan yana fitar da duk wani datti dake gabanki kuma yana sa gabanki yayi laushi. Saidai a wasu lokutan, farin ruwa me kauri na iya zama alamar rashi lafiya. Masana kiwon lafiya sun ce a ya...

Kalar ruwan infection

Gaban mace
Ruwan infection dake fitowa daga gaban mata yana da kaloli da yawa. Wanda ba na infection ba, fari ne me yauki. Amman ruwan infection, yakan iya zama da kalar Green ko a ce ruwan kore ko kalar ganye. Fitowar ruwa kalar ganye,ko ace green ko ace kore, yana iya zama alamar cutar sanyi wadda akan dauka lokacin jima'i ko a bandaki mara tsafta. Hakanan irin wannan ruwa kan iya zama matsalar cutar yoyon fitsari. Sai kalar Grey/Gray ko ace kalar ruwan toka ba me duhu ba. Idan kika ga ruwa me kalar Grey/Gray ko kalar ruwan toka ba me duhu ba a gabanki to alamar cutace, musamman idan ya zamana kina jin zafi lokacin da kike fitsari. Yawanci antibiotic suna maganin irin wannan matsalan, amma idan ya tsananta a tuntubi likita. Ruwa me kalar ja ko kalar Yellow, ruwan dorawa, ko ...

Yaya kalar ruwan ni’ima yake

Gaban mace
Ruwan ni'ima yana zuwane a yayin da sha'awar mace ta motsa. Kuma yana zuwane dan ya sa a ji dadin jima'i, shi namiji ya ji dadin yin jima'in hakanan itama macen ta gamsu. Ruwa ne fari kuma me yauki. Kuma yana saurin bushewa ko bacewa. Shi wannan ruwa yana taimakawa wajan wanke gaban mace da kuma sawa yayi santsi, watau idan namiji zai yi jima'i da ita, wannan ruwa zai sa mazakutarsa ta shiga cikin farjin macen cikin sauki da jin dadi ba tare da amfani da yawu ko wani mai ba. Macen da bata da irin wannan ruwa, ko kuma babu shi isashshe, shi yasa ake amfani da abinda ake cewa Lubricant, wanda mai ne dake sa mazakuta ta shiga farji ba tare da matsala ba ko jin zafi, akwai wanda ake sayarwa a shaguna, amma ana amfani da man zaitun ko man kwakwa duk sun iya yin wannan aiki. S...