Friday, December 5
Shadow

Rahotanni sunce Shugaba Tinubu ya fara neman wanda zai nada a matsayin sabon Ministan kudi, bayan da Ministan Kudi Wale Edun ya samu rashin lafiyar Shanyewar rabin jiki

Rahotanni sun ce tuni shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara neman wanda zai maye ministan Kudi, Wale Edun dashi.

Ministan Kudi, Wale Edun ya kwanta rashin lafiya bagtatan inda rahotanni suka ce shanyewar rabin jiki ce ta kamashi.

Rahotannin sun ce an garzaya dashi zuwa kasar waje.

Hakanan rahotannin sun ce ko da ya warke da wuya ya iya komawa bakin aikinsa.

Wannan ne yasa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya fara meman wanda zai maye gurbinsa dashi.

Rahotanni sun ce Shugaba Tinubu ya baiwa Gwamnan Babban bankin Najeriya, CBN umarnin maye gurbin Ministan kudin a wai taro da za’a yi a kasashen waje.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Gwamnan jihar Naija ya jawo cece-kuce sosai bayan da aka ganshi ya shiga coci an yi irin addu'ar kiristoci dashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *