
Wakar da shahararren mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara yawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a ziyarar da ya kai jihar Katsina ranar Juma’a ta dauki hankula sosai.
A cikin wakar an ji Rarara yana hadawa hadda Yarbanci.
A yayin da yake wakar, an ga Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna tafawa Rarara.
Da yawa sun jinjinawa Rarara inda suka ce wakar ta yi dadi.