
Rashin tsayayyiyar wutar lantarki na tsawon lokaci na sama da kwanaki 10 ya jawo dakatar da kasuwanci a cikin ƙwaryar birnin Kano da kewaye.
Wasu mazauna Kano da suka zanta da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a ranar Lahadi, sun koka game da rashin sanin tabbacin abin da za su yi bayan faɗuwar babban layin wutar lantarki wanda ya jefa al’umma cikin duhu da shafar kasuwanci da al’umma a gidajensu.
Da yawa daga cikin ‘yan kasuwa sun koka game da illar rashin wuta ga kasuwancinsu.
Wani mai gidan otel da unguwar Sabon Gari da ke ƙaramar hukumar Fage, Jude Michael, ya ce yana cikin tashin hankali.
Michael ya ce ya rasa kwastamominsa sakamakon rashin wuta da yake amfani da ita wajen ajiye kayan abin sha.
“Na shafe tsawon kwanaki ina aiki da Janareta kuma har ya fara taɓa kuɗin kasuwancina wanda ka iya zama asara.
“A wasu lokutan kwastamomina kan zo, a wasu lokutan kuma zai in ji shiru. Gaskiya hakan na sagar da guiwata,” ya faɗa.
Wani mai sana’ar walda a unguwar Dakata da ke ƙaramar hukumar Nassarawa, Abubakar Bala, ya ce, yana dogara ne da man dizal wajen gudanar da ayyukansa duk da ya san ba abu ne mai ɗorewa ba.
“Mun biya kuɗin wuta, sai dai ba ma samun wutar. Idan dai ba a dawo da wuta ba, kasuwancina zai iya durƙushewa.”
Bala ya buƙaci gwamnati da ta gaggauta gyara wutar da kuma samar da ƙarin hanyoyin samar da makamashi.
Shi ma wani mai sana’ar walda a ƙaramar hukumar Tarauni, Aminu Sani, ya ce ya dakatar da yin sana’arsa saboda tsadar mai da ake buƙata wajen kunna janareta.
“Mun fi cazar mutane kudi idan da janareta muka yi musu aiki, sai dai ba kowa ne yake iya biyan kuɗin da za mu caza ba. Wannan ta sa a yanzu muna zaune ne babu aiki.”
Shi ma wani mai sana’ar sai da abincin da aka tanana da ke kan titin Zari’a a Kano mai suna Manu Garba, ya ce, a halin yanzu da yawan masu irin wannan sana’a tasu ba shi ya taran musu a ka saboda ƙoƙarin da suke na kauce wa asara ta hanyar samar da wuta gudun kar kayayyakinsu su lalace.
“Muna sa ran samun kasuwa sosai a lokacin wutun Easter da samun riba ko da ‘yar kaɗan ce saboda yanayin tattalin arziƙin ƙasar nan. Amma saboda rashin tsayayyiyar wuta ta jawo sai ma bashi da ake bin mu.”
“Mun yi asarar kaji da kifi ƙanƙararru kwali-kwali a cikin mako ɗaya a yayin da wasu daga cikinmu abin a nan ya tsaya, wasu kuma sun yi asarar da ta fi haka.”
Wata mata mai sana’ar gyaran gashi, Bunmi Ola, ta yi ƙorafi game da rashin wuta wanda ya jawo wa ‘yan kasuwa da yawa cin bashi.
Ta ce wannan babban ƙalubale ne ga waɗanda kasuwancinsu ya dogara ne da wutar lantarki.
Mis Ola, ta ce, duk da irin mawuyacin halin da suke ciki na raɗaɗin asarar da suka yi, kamfanonin rarraba wutar na cigaba da kawo takardar biyan kuɗin wuta.
Sai dai masu sana’ar cajin waya sun ce su kasuwancinsu gaba ya ci, ba baya ba.
Wani daga cikin masu irin wannan sana’a, Isa Umar, ya ce, ya ƙara kuɗin kayansa saboda tsadar mai inda yake cazar Naira 150-200 na cajin kowacce waya ɗaya.
Haka kuma rashin wutar ya jawo ƙarancin ruwa a faɗin jihar Kano a yayin da ake sayar da jarkar ruwa mai nauyin lita 25 a kan Naira 100-200 a wasu yankunan Kano.
Sani Bala, wanda shi ne jami’in yaɗa labarai na kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano, ya ce, ƙarancin wutar na faruwa sakamakon gyare-gyare da ake yi.
Bala ya ce aikin gyaran ya zama dole ne domin inganta kayan da ake amfani da su da kuma tabbatar da lafiyar injiniyoyin da ke aiki.
Ya ce, aikin inganta kayayyakin ana yi ne domin tabbatar da samar da wuta mai ɗorewa daga kamfanonin rarraba wutar da yya haɗa da samar da wuta na tsawon lokaci da hidimta wa al’umma yadda ya kamata.