
Rahotanni sun bayyana cewa, ribar da bankunan Najeriya ke samu ta ragu matuka a yayin da suka bayyana yawa kudaden da suka samu a watanni 3 na farkon shekarar nan.
A baya dai bankunan kan sau jimullar ribar Naira biliyan 150 a iin wannan lokaci amma da alama lamura sun canja.
An alakanta hakan da hauhawar farashin kayan masarufi inda a yanzu bankunan ke kashe kudade da yawa wajan gudanar da ayyukansu fiye da da.
Misali bankin GTCO ya samu raguwar riba da kaso 41 cikin 100, shi kuma bankin First Bank ya samu raguwar riba ne da kaso 20.2 cikin 100.
Da dai sauransu.